
Babban limamin babban masallacin zuba, yahaya ibrahim yana jagorantar sallah a ranar Laraba
Agora na Zuba a ƙaramar hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya, Alhaji Muhammed Bello Umar, ya buƙaci manoma da makiyaya su ci gaba da zama lafiya da juna.
Alhaji Umar ya yi wannan kiran ne jim kaɗan bayan ya bi sahun sauran al’ummar musulmi su gudanar da sallar idin bana a filin Idi da ke Zuba ranar Laraba.
Ya kuma jaddada buƙatar manoma da makiyaya su zauna lafiya cikin lumana, inda ya ce za a samu zaman lafiya da haɗin kai ne kawai idan aka yi haƙuri.
Ya kuma buƙaci shuwagabannin unguwanni, ƙauyuka da al’ummomi a faɗin masarautar da su wayar da kan al’ummarsu kan muhimmancin ɗorewar zaman lafiya a tsakanin ƙabilu.
Ya ce, “Kamar yadda manomi ke mutunta amfanin gonakinsa, haka ma Bafulatani yake daraja shanunsa, don haka su biyun su yi haƙuri da juna domin a samu zaman lafiya.”
Ya kuma jaddada cewa wajibi ne musulmi su yi amfani da bukukuwan Ƙaramar Sallah wajen yin koyi da koyarwar Manzon Allah (SAW), kamar yadda ya buƙace su da su ci gaba da zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da ɓangaranci, ƙabilanci da addini ba.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar sun tura ‘ya’yan su domin samun ilimin addinin Musulunci da na boko, inda ya ce ilimi shi ne ginshikin al’umma.