Back

Ƙaramar Sallah: Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata da Laraba ranakun hutu

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Ƙaramar Sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Aishetu Ndayako, ta fitar ranar Lahadi.

Ministan ya taya ɗaukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma.

Tunji-Ojo ya yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan ɗabi’u da ke tattare da kyautatawa, soyayya, haƙuri, zaman lafiya, kyakkyawar maƙwabtaka, tausayi, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Sallama) ya yi misali da shi.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ayyana ranakun Talata 9 da Laraba 10 ga Afrilu, 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Ƙaramar Sallah.

“Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, yana taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.

“Tunji-Ojo yana kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan ɗabi’u waɗanda suka haɗa da kyautatawa, soyayya, haƙuri, zaman lafiya, kyakkyawar maƙwabtaka, tausayi kamar yadda Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wa Sallama) ya yi misali da shi.

“Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da haɗin kai domin ingantawa da samun zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar.

“Ministan yana yiwa ɗaukacin al’ummar Musulmi barka da Sallah tare da addu’ar aminci, albarka, da tagomashin Allah su kasance da kowa da kowa da kuma ƙasar mu baki ɗaya.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?