Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta baza jami’ai na yau da kullum da na musamman, da kuma motocin sintiri, da motocin dauƙar marasa lafiya, domin gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
Shugaban Hukumar FRSC, Dauda Ali-Biu, wanda Mataimakin Shugaban Rundunar (DCM) mai kula da ayyuka, Shehu Zaki, ya wakilta, ya bayyana haka a wajen ƙaddamar da Babban Gangamin Bikin Sallah na shekarar 2024 a ranar Asabar a Abuja.
Ali-Biu ya kuma ce, an kuma baza manyan motocin jan motoci da babura, inda ya ƙara da cewa an tura dakarun ne a manyan tituna 52 na ƙasar nan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa taken gangamin na shekarar 2024 shi ne “Yin Lodi fiye da Ƙima Bam Mai Lokaci ne: A Dakatar da Mutuwa, Kar a yi Lodin Mutane, Dabbobi ko Kaya fiye da Ƙima”.