Back

Ƙaramar Sallah: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai da su fara duban sabon watan Shawwal ranar Litinin

Alhaji Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA).

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasa (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar, ya umurci al’ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Shawwal 1445AH daga ranar Litinin mai zuwa.

Farfesa Sambo Janaidu, Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Al’amuran Addini na Majalisar Sarkin Musulmi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Sakkwato ranar Lahadi.

Bayanin ya ci gaba da cewa: “Ana sanar da al’ummar Musulmi cewa ranar Litinin 8 ga Afrilu, daidai da 29 ga watan Ramadan 1445AH, ita ce ranar neman jinjirin watan Shawwal 1445AH.

“Saboda haka ana buƙatar musulmi da su fara neman jinjirin watan Shawwal 1445AH a ranar Litinin kuma su kai rahoto ga Hakimin Ƙauye mafi kusa don tuntuɓar Sarkin Musulmi.

“Bugu da ƙari, jama’a na iya bayar da rahoton ganin watan ta hanyar lambobin waya kamar haka: 08037157100, 07067416900, 08066303077, 08036149757, 08035965322, da 08099945903.

Sarkin Musulmi ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da taimakon Musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa watan Shawwal, wata na 10 na kalandar Musulunci, yana biyo bayan watan Ramadan, a daidai lokacin da aka fara bikin Ƙaramar Sallah.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?