
Tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
A yau Alhamis ne aka ci gaba da shari’ar tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, a gaban Mai Shari’a Hamza Mu’azu na Babbar Kotun Birnin Tarayya.
An gurfanar da Emefiele a gaban Mai Shari’a Mu’azu ne bisa tuhume-tuhume 20 waɗanda suka haɗa da cin hanci da rashawa, haɗa baki, cin amana, yin jabu, da kuma samun sa da dala miliyan 6,230 ta hanyar ƙarya.
A ci gaba da sauraren ƙarar, wani ƙwararren mai bincike ya tabbatar da cewa an yi jabun wata takarda da aka yi amfani da ita wajen neman biyan dala miliyan 6.2 don masu sa ido kan zaɓe na ƙasashen waje.
Shaidan, Bamaiyi Meriga, wanda Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kira, ya shaida wa kotun cewa bayan binciken ƙwaƙwaf da aka yi a kan takardun da ake jayayya a kai, ya gano cewa akwai ƙwararan hujjoji na yin jabun sa hannu, inda ya ƙara da cewa tambarin zartar da hukuncin ya sha bamban da na asalin.
Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ba ne.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Mu’azu ne ya amince da karɓar wasu takardu guda biyu da suka haɗa da umarnin Shugaban Ƙasa kan masu sa ido na ƙasashen waje, cikin shaida.
A yayin da lauyan Emefiele ya yi masa tambayoyi, shaidan ya ce shi ba ma’aikacin EFCC ba ne, kuma hukumar ba ta biya shi ba amma shi ma’aikacin Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ne.
Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda shaidan ya kasance, inda ya ce shaidan ya yaudari kotu ta hanyar guje wa tambayoyi.
Sai dai lauyan masu ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji daɗin iƙirarin da lauyan wanda ake tuhuma ya yi ba.
An ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 11 ga Maris.