Shugaban Kwamitin Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sanda (PCRC), Mogaji Olaniyan, ya yi kira da a gaggauta magance abin da ya kira ƙiyayya ga jami’an ‘yan sandan Nijeriya.
Olaniyan ya bayyana lamarin a matsayin mai ban tsoro, yana mai nuna cewa ƙiyayyar ta kasance cikin abubuwan da ke shafar tsaron ƙasar.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin bikin kwamitin karo na 40 da aka gudanar a Abeokuta.
Olaniyan, wanda ya yi Allah-wadai da wannan ƙiyayya da ta yaɗu, ya ce PCRC na ƙulla alaƙa ta dindindin a tsakanin al’umma da ‘yan sanda domin kawo ƙarshen wannan mummunan lamarin.
Ya kuma jaddada cewa dole ne a magance wannan ƙiyayyar don samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin jama’a da ‘yan sanda, tare da samar da tsaro a faɗin ƙasar nan.
Olaniyan ya ce “Muna kira ga mutane da su so ‘yan sandan Nijeriya, wannan ne abinda suka rasa. Tun muna yara mun haifar da ƙiyayya tsakanin yaran mu da ‘yan sandan Nijeriya.
“Wannan ƙiyayya ta fara ne daga gidajenmu. Misali idan iyaye suna so su tsawatar wa ’ya’yansu za su ce ‘Zan kira muku ‘yan sanda’. Wannan shi ya sa yaranmu suka girma da ƙiyayya ga ’yan sanda kuma shi ya sa muke ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan lamarin.”
Shugaban Kwamitin na Jihar, Samson Kunle Popoola, ya bayyana cewa, har yanzu tsaron Jihar Ogun yana da muhimmanci ga hukumar PCRC, don haka kwamitin da kyakkyawar alaƙa da ‘yan sanda.
Ya tabbatar da cewa Jihar Ogun ta kasance jiha mafi zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya, yana mai kira da a ƙara samun haɗin kai tsakanin mazauna yankin da ‘yan sanda domin kiyaye hakan.