A ranar Alhamis ne ƙudurin dokar dawo da taken Nijeriya da aka ɗauka lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, 1960 ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa.
Wannan ya biyo bayan gabatar da ƙudirin ne da ɗan Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta tsakiya) ya yi a zaman majalisar.
Kafin zartar da shi, Sanatocin sun gudanar da zaman zartaswa na kusan sa’o’i biyu wanda Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya jagoranta.
Bayan an zartar, Akpabio ya miƙa ƙudurin dokar ga Kwamitin da ke Kula da Al’amuran Tarayya da na Gwamnatocin Tarayya, ya kuma buƙaci da ya miƙa rahotonsa ga kwamitin baki ɗaya da wuri.