
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilan da suka sa aka jinkirta rabon hatsin da ya kai tan dubu arb’a’in da biyu kyauta ga ‘yan Najeriya domin shawo kan matsalar karancin abinci a halin yanzu.
Za a iya tunawa cewa Ministan Noma a ranar takwas ga wannan watan ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta raba gero, masara da sauran kayayyakin abinci ga marasa galihu a Najeriya don magance wahalhalu.
Sai dai kusan makwanni uku ba a baiwa ‘yan Najeriya wani hatsi ko kayan abincin ba saboda matsalar tattalin arzikin kasar ya yi katutu, ga tsadar kayan abinci.
Da yake bayyana jinkirin, mai bawa shugaban kasa Tinubu shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce ana ci gaba da yin buhunan hatsi a wurare bakwai masu muhimmanci a kasar nan.
Onanuga ya kuma ce Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta dauki nauyin buhunan hatsin da nan ba da dadewa ba za a rabawa ‘yan Najeriya marasa galihu.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya kara tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su samu hatsin kyauta.
Onanuga ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta samar da shinkafa tan dubu sittin domin baiwa ‘yan Najeriya.
“An killace hatsin a wurare bakwai, yanzu ana yin buhuna domin isar da su ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA). Bukatar zuba hatsin a buhun ya haifar da tsaiko saboda sabbin odar da gwamnati ta yi wa buhunan.
“Yan Najeriya ba za su biya kuɗin hatsin ba, saboda da kyauta za a raba.
“Wanda za a kara shi ne tan dubu sittin na nikakkiyar shinkafa da Gwamnatin Tarayya za ta saya daga Mega Rice Millers.
Ya ce, tuni, aka fara samun ragin farashin kayan abinci tun daga lokacin da gwamnati ta sanar da cewa zata raba kayan abincin kyauta, ya kara da cewa lokacin raba kayan na gabatowa. An samu raguwar farashin kayayyaki a manyan kasuwannin hatsi a kasar.