Back

Ƙungiya ta raba wa gidaje sama da 270 kayan abinci a Kaduna

Wata Ƙungiya Mai Zaman Kanta (NGO) mai suna Hope for the Village Child Foundation (HVCF) ta raba kayan abinci da kuɗinsu ya kai naira miliyan 3 ga ƙananan yara da mata sama da 270 a cikin al’ummomin jihar Kaduna a ƙoƙarinta na rage matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar.

Mataimakiyar Daraktan HVCF, Rabaran Juliana Ekwoanya, a yayin rabon kayayyakin a Kaduna a cibiyar HVCF, ta bayyana cewa wannan shiri na daga cikin ayyukan da suke yi na taimaka wa marasa galihu don rage wahalhalu.

A cewarta, manufar ita ce samar da muhimman kayan abinci ga mabuƙata musamman mata da yara da kuma rage yunwa a cikin al’umma.

Ta yi nuni da cewa, ana sa ran kayayyakin abincin za su taimaka wajen daƙile illar matsalar tattalin arziƙi ga rayuwar waɗanda suka amfana.

Sai dai ta koka kan matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a cikin al’umma, inda ta ce akwai buƙatar a yi aiki da yawa kan matsalar ƙarancin abinci a ƙasar.

Ekwoanya ta ce, “wannan ƙoƙarin agaji ba wai kawai yana bayar da agajin gaggawa ba har ma yana samar da jin daɗin jama’a da goyon baya, yana taimakawa wajen samar da al’umma mai ƙarfi, mai tausayi da ke kula da mafi raunin jama’ar ta”.

Ta ci gaba da cewa ta hanyar rarraba kayan abinci, waɗanda suka ci gajiyar za su samu abinci mai gina jiki kuma za su iya biyan buƙatunsu na abinci.

Mataimakiyar Daraktan ta kuma buƙaci ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da gwamnati da su taimaka wa masu buƙata, tana mai cewa akwai buƙatar a ɗauki matakin gaggawa kan matsalar ƙarancin abinci.

A cewarta, kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa 100kg 100, wake 100kg 100, masara 100kg buhu 10, albasa 5, katan biyu na maggi da gishiri duka na miliyan 3.

Ta ƙara da cewa waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun fito ne daga ƙananan hukumomin Chikun, Igabi da Kajuru na jihar.

Wani matashi mai shekaru 15 mai suna Miracle Musa wanda ya yi magana a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin ya yaba wa HVCF saboda tallafin su da ayyukan jin ƙai.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?