Back

Ƙungiya za ta gina gidaje 370,000 a faɗin Nijeriya

Wata ƙungiya mai zaman kanta ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Cibiyar Ƙarfafawa da Kula da Ƙalubalen Rayuwa ta Duniya (GECLC), ta ce ta kammala shirye-shiryen gina gidaje 370,000 a faɗin Nijeriya domin magance matsalolin gidaje da jama’a ke fuskanta.

A cewar Cibiyar, matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin cimma lamba 9 Ƙirƙira da Ababen More Rayuwa na Muradun Ci Gaba Mai Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya (SDGs) da lamba 11 Birane da Al’ummomi Masu Ɗorewa a Nijeriya nan da 2030.

Da yake jawabi a taron ƙaddamar da aikin a Kaduna ranar Asabar, Shugaban Cibiyar Amb. Vincent Ejikeme Agbo, ya ce a ƙarƙashin aikin, za a gina gidaje 10,000 a kowace jiha cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya a matakai biyu.

Agbo ya ƙara da cewa, aikin, wanda nan gaba kaɗan za a faɗaɗa shi zuwa wasu ƙasashen Afirka, an fara shi ne a Nijeriya, domin bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙi da tallafawa ƙoƙarin ci gaban Gwamnatin Tarayya da na jihohin ƙasar nan.

A cewar Shugaban GECLC, “Manufofinmu a Cibiyar Ƙarfafawa da Kula da Ƙalubalen Rayuwa ta Duniya, sun yi daidai da Muradun Ci Gaba Mai Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya (SDG).

“Babban burinmu a nan shi ne samar da ingantattun gidaje masu araha ga mutane masu shekaru da matsayi daban-daban.

“Ba mu yi alƙawarin aljanna a duniya ba amma birane masu daraja a duniya waɗanda za su kasance cikin mafiya kyau wajen kyawu, abubuwan more rayuwa, tsaro da kwanciyar hankali.

“A makonnin da suka gabata, mun je Asaba, Jihar Delta, don ƙaddamar da wannan gagarumin aikin tare da haɗin gwiwar ɗaya daga cikin ‘yan kwangilar mu; Frankly Royal View Limited. Domin sanya gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 da kuma mai girma Ministan Babban Birnin Tarayya domin samar da muhimman abubuwa, musamman filaye domin gudanar da waɗannan manya-manyan ayyuka a jihohin, ni da tawaga ta mun fara tattaunawa da su.”

Da yake bayyana dalilin da ya sa aka baiwa Jihar Kaduna fifiko, ɗan ƙungiyar, Amb. Larry-Goodwill Ajiola (Ph.D) ya ce, “Kaduna ita ce jiha ta farko da ta amince da wannan aiki a faɗin ƙasar nan, don haka Jihar Kaduna ita ce ta ɗaya a wannan aikin. Kaduna jihar mu ce, sun ba mu izini kuma a shirye suke su ba mu filaye da tallafa mana ta fuskar fasaha da kuɗi don ganin an samu nasara.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?