Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya bayyana rashin amincewa da tsarin sabon kwamitin kan mafi karancin albashi Wanda Gwamnatin Tarayyar ta kafa.
Ajaero, wanda ya yi magana jiya a taron sasantawa da sasanta ma’aikata karo na biyu a Abuja, ya ce kwamitin na aiki da gwamnoni da tsofaffin gwamnoni, musamman wadanda ba za su iya biyan mafi karancin albashi na Naira dubu talatin a jihohin su ba.
Taron wanda kungiyar tuntubar ma’aikata ta Najeriya (NECA) ta shirya yana da taken: “Karfafa Ra’ayin bangarori uku da Tattaunawar Zamantakewa don Dorewar Tsarin Masana’antu a Najeriya”.
Shugaban ƙwadagon ya ce hakan na nuni da rashin daidaituwa da kuma matattun tsari kan ingantacciyar tattaunawa ta zamantakewa kan sabon albashin ma’aikata.
Ya ce, “Hatta ma’aikatu masu zaman kan su ba sa biyan albashin, jihohi ba sa biya, sannan a kwamitin mafi karancin albashi, ka je ka kawo duk gwamnonin da ba su biya mafi karancin albashi na dubu talatin ba. Me za su gaya musu? Wannan maganar matattciya ce tun daga idowar ta..”
Ajaero ya kuma yi magana kan illar hauhawar farashin kaya ga ma’aikatan Najeriya, inda ya kara da cewa, Ko nawa za a biya ma’aikaci, a yanayin tattalin arzikin Najeriya, nan da shekaru biyar masu zuwa, ba zai iya sayen buhun shinkafa ba.
Ya ce akwai bukatar a sake duba dokar da ta tanadi tsawon shekaru biyar-biyar na sake tattaunawa a kan mafi karancin albashi na kasa domin yi dokar kwaskwarima ta ba da damar sake fuba lamarin duk shekara-shekara bisa la’akari da hauhawar farashin kayayyaki da kuma darajar Naira.
Ajaero ya kuma ce ma’aikata ba su ji dadin yadda gwamnati ke aiwatar da aikin bayar da albashin ma’aikata ba, yana mai cewa babu wanda ke biyan Naira dubu talatin da biyar kamar yadda aka amince a bara.
Amma sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa sabon mafi karancin albashin zai kasance mai adalci, dawwamamme da kuma amfani ga dukkan masu ruwa da tsaki.
Akume, wanda ya samu wakilcin Richard Pheelangwah, ofishin majalisar zartarwa a ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da fahimtar juna tsakanin gwamnati, masu daukar ma’aikata, da kungiyoyin kwadago da bullo da sababbin hanyoyin magance matsalar mafi ƙarancin albashi, ya Kuma zamo mai ɗorewa kuma mai dorewa.
Ya ce ta hanyar amfani da hanyoyin yanke hukunci yadda ya kamata, masu ruwa da tsaki za su iya gudanar da shawarwarin mafi karancin albashin da ke tafe cikin hikima, fahimta, da kuma kudurin tabbatar da dorewar tsarin huldar masana’antu a Najeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya kara bayyana kokarin da gwamnati ke yi na dakile wahalhalun tattalin arzikin kasa da ‘yan Najeriya ke fuskanta, kamar kara zuba jari a bangaren ababen more rayuwa, hanyoyin sufurin jama’a da iskar gas, hanyoyin jiragen kasa da na ruwa, da fadadawa da karfafa hanyoyin kare lafiyar jama’a, kamar tsarin musayar kudi da ya dace. da sauransu.
Shugaban NECA, Taiwo Adeniyi, ya ce taron zai samar da yanayi mai kyau don tattaunawa mai ma’ana da masana kan mahimmancin hanyoyin warware takaddama da ke tabbatar da hakki da jin dadin ma’aikata tare da tallafawa ci gaba mai dorewa da ci gaban kasuwanci.