Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC, a jiya ta yi zargin yunƙurin gwamnatin tarayya na yi mata zagon ƙasa ta hanyar raba kan jama’a, inda ta ce an dakatar da zanga-zangar ta kwanaki biyu saboda barazana da kuma tsoratarwa.
Har ila yau, ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin tarayya ta mamaye hedikwatarta da kuma ofisoshin jihohi da sojoji a faɗin ƙasar, inda ta ce ba za a tsoratar da mambobin majalisar da wata barazana ba.
Haka ma dai shugabannin ƙungiyar ƙwadagon sun sha alwashin ba za su mutunta duk wata gayyata da gwamnatin tarayya za ta yi musu na halartar duk wani taron dare ba, gabanin duk wani mataki da ta ayyana a faɗin ƙasar, yana mai cewa dabara ce ta yaudarar su.
Shugaban ƙungiyar ta NLC, Joe Ajaero, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a wani taron ƙarawa juna sani na ‘yan Najeriya a gidan ƙwadago da ke Abuja, ya ci gaba da cewa shugabannin NLC za su halarci taron da jami’an gwamnati ne kawai idan ba a ayyana wasu matakai ba.
Ya ce: “Duk lokacin da suka gayyace mu taro, za mu halarci kuma mu saurare su domin idan ba mu halarta ba, za su yi mana barazana. Kuna sane da cewa sun yi taro da mu har zuwa yammacin ranar Lahadi. Yayin da ake wannan taron, sun rubuta wasiƙu ga duk ƙungiyoyi don su yi mana zagon ƙasa.
“Kuna ganawa da shugabannin NLC, kuma har yanzu kuna gayyato kowace ƙungiya a ƙasar nan domin ku yi mana zagon ƙasa. Ko a wancan taron da nake magana, sun so mataimaka na biyu su yi magana, don kada mu samu shugabanni, amma duk da haka mun tsira.
“Babu wani abu a doron ƙasa da ba su yi ba na ruguza NLC. Babu komai! Kuma har yanzu muna ƙara ƙarfi. Don haka idan suka gayyace mu taro, za mu je mu saurare su domin muna da ra’ayinmu, muna da matsayarmu, kuma za mu gabatar da matsayinmu a hankali. Ba za mu ce ba za mu je ba sai lokacin da muka fahimci…”
Ku tuna cewa sa’o’i kaɗan gabanin fara zanga-zangar ta kwanaki biyu, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, ya gayyaci shugabannin Ƙungiyar zuwa wani taro da ya ɗauki tsawon dare a wani mataki na daƙile zanga-zangar.
Ajaero ya bayyana taron dare na ranar ashirin da shida ga watan Fabrairu a matsayin “tsohuwar dabara” da gwamnatin tarayya ta ɗauka don jinkirtawa, tarwatsa masu zanga-zangar da kuma karya ƙarfin gwuiwar masu zanga-zangar a faɗin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar ƙwadagon, yayin da yake amsa tambayoyin, ya ce: “Daga yanzu, NLC ba za ta ƙara jin daɗin halartar taruka ba a jajibirin kowane mataki. Kar a sake! Ɓata lokaci ne da ɓata kuzari kuma babu abin da ke fitowa daga irin waɗannan tarurruka.
“Wannan shi ne don a jinkirta mu, a tarwatsa mu, da kuma sa mutane su ji cewa mun je can ne don tattauna wasu batutuwa, baya ga batutuwan da suka shafi ƙasa. Wannan shine sabon ƙudurinmu.
“Ku (gwamnatin tarayya) ba za ku iya kiranmu taro ba idan muna da wani mataki gobe ko jibi, kuma ku jinkirta mu har zuwa ƙarfe sha ɗaya na dare, ƙarfe sha biyu na dare, don kada mu fito mu yi gangamin ɗaukar mataki. Wannan tsohuwar dabara ce. Ina ganin ya kamata su rungumi sabbin dabaru.”
Ajaero, wanda ya ke tsakanin Femi Aborisade, da sauran shugabannin ƙungiyar ƙwadago, har ila yau, ya yi zargin cewa jami’an gwamnati a lokuta daban-daban sun yi ƙoƙarin yin amfani da dabarar raba kai don su yi wa NLC zagon ƙasa, haɗe da ci gaba da aika wasu samari domin su yi zanga-zanga a jiya (Talata).
Ya kuma ce gwamnati na son karya yarjejeniyoyi da dokokin ƙasa, kuma ɗaya daga cikin misalan shi ne rashin aiki na matatar mai ta Fatakwal da aka sanar za ta fara aiki a watan Disambar da ya gabata.
“Ina nan lokacin da Shugaba Tinubu ya tambayi Ƙaramin Ministan Mai, Heineken Lokpobiri, game da lokacin da matatar man za ta yi aiki. A yayin da muke magana yanzu, babu ɗigon mai ko fetur da ya samu daga wannan matatar! Su daina yiwa mutane ƙarya,” in ji Ajaero.