Back

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya ta yi watsi da harajin da CBN ya saka na tsaron yanar gizo

Shugaban NLC, Mista Joe Ajaero

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi watsi da umarnin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayar na sanya harajin kaso 0.5 (0.005) na tsaron yanar gizo kan kuɗaɗen da abokan ciniki ke turawa.

Mista Joe Ajaero, Shugaban NLC ne ya bayyana matsayin NLC a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Talata a Abuja.

Ajaero na mayar da martani ne kan wata sanarwa da CBN ya fitar a baya-bayan nan, inda ya umarci bankuna da masu gudanar da ayyukan biyan kuɗi da su aiwatar da cire harajin, wanda zai fara aiki nan da makonni biyu.

CBN ya ce matakin, ‘wanda ake ganin da nufin ƙarfafa matakan tsaron yanar gizo, na barazanar ƙara matsalar kuɗi da jama’a ke fuskanta.

Ajaero ya ce NLC ta yi Allah-wadai da wannan umarni don haka ta yi kira da a gaggauta dakatar da sauya manufar.

A cewarsa, wannan harajin da za a aiwatar da shi, wani nauyi ne ga ‘yan Nijeriya masu aiki tukuru.

“Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya ta fahimci mahimmancin tsaron yanar gizo a zamanin yanar gizo na yau.

“Duk da haka, sanya irin wannan haraji kan kuɗaɗen da ake turawa, ba tare da la’akari da tasirinsa ga ma’aikata da kuma sassan al’umma masu rauni ba, bai dace ba.

“Wannan harajin wani haraji ne da ya yi wa ‘yan Nijeriya yawa, yana ƙara musu nauyin kuɗi.

“Muna ganin wannan harajin a matsayin wani haɗin gwiwa na masu mulki don ci gaba da karɓar kuɗi da ƙarfi da ci da gumin ma’aikata marasa galihu da talakawa,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?