Back

Ƙungiyar Ƙwadago ta rage ƙarin mafi ƙarancin albashin da ta nema zuwa naira 500,000

Ƙungiyar Ƙwadago a ranar Laraba ta rage mafi ƙarancin albashi daga naira 615,000 da ta nema da farko zuwa naira 500,000 bayan an kasa cimma matsaya a taron Kwamitin Uku na ranar Talata.

Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, Farfesa Theophilus Ndubuaku, ne ya bayyana hakan, inda ya shaida cewa an tilasta wa Ƙungiyar Ƙwadagon ta rage buƙatar ta domin ganin Gwamnatin Tarayya ta cimma wannan tsari.

Ya ce, “Eh, gaskiya mun rage shi zuwa naira 500,000. Amma har yanzu ba mu samu ci gaba ba a halin yanzu.”

Ndubuaku ya shaida a ranar Talata cewa, ƙungiyar ƙwadago ta yi matuƙar mamakin yadda gwamnati ba ta nuna tausayi ba duk da sanin cewa talakawa na kokawa kan halin ƙunci da hauhawar farashin kayayyaki da manufofinta suka haifar.

Da aka tambaye shi game da mataki na gaba idan ba a cimma matsaya a taron na Laraba ba, ɗan ƙungiyar ya bayyana cewa za su iya komawa su gaya wa ma’aikatan Nijeriya da ke cikin damuwa su zauna a gida har sai Gwamnatin Tarayya ta zo da wani tayin da za a amince da shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?