Manhajar shirin bayar da lamunin ɗalibai da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu yake shirin ƙaddamarwa a ranar ashirin da ɗaya ga watan biyu na wannan shekarar ya samu naƙasu, yayin da Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta Ƙasa, NANS, ke neman a ɗage taron, bisa zargin an yi watsi da ra’ayin ɗalibai.
Binciken da jaridar Vanguard ta yi ya nuna cewa, Sakataren Zartaswan shirin bai samu damar ganawa da shugabannin ƙungiyar daliban don sauraren nasu ra’ayin kan yadda ya kamata a zartas da shirin ba.
Daliɓan sun bayyana lamarin a matsayin ƙoƙarin aske kan mutum ta bayan shi.
Da aka tuntuɓi Shugaban NANS na ƙasa, Kwamared Lucky Emonefe ta wayar tarho, ya shaida wa wakilin Vanguard cewa ƙungiyar za ta miƙa wa shugaban ƙasa takarda kunshe da bayanai kan matsayar ta dangane da lamarin.
Emonefe ya ce, “Eh, ba mu ji daɗin yadda waɗanda ke da alhakin gudanar da shirin ke tafiyar da lamarin ba. Har ya zuwa yanzu, Sakataren Zartaswar shirin bai gana da dalibai ba domin jin ta baki su kan yadda suke so tsarin ya gudana. Muna rubutawa shugaba Bola Tinubu wasiƙa cewa a dakatar da ƙaddamar da manhajar.”
“Muna miƙa wasiƙa ga Shugaban Ƙasa kuma muna son mai Girma shugaban ƙasar ya saurare mu, ya kuma dakatar da ƙaddamar da manhajar. Ba za ku iya samun nasara a tsarin da kuke shirin yi domin kyautatawa dalibai ba, ba tare da kun shigo da su cikin shirin su ma dun bsda ta su gudunmuwar ba,. Za mu nemi a dakatar da ƙaddamarwar har sai an lura da abin da muka lura cikin shirin,” in ji shi.
Emonefe, ya kuma ambata cewa NANS bata yarda da haɗawa da ɗalibai a manyan makarantu masu zaman kansu a matsayin masu cin gajiyar ba.
“Idan mutum zai iya tura dan shi jami’a mai zaman kan ta inda ake karɓar sama da Naira miliyan ɗaya a matsayin kuɗin makaranta. Me zai sa irin wannan mutum ya fara fafatukar neman rancen da bai wuce dubu dari biyu ba? Irin wannan tallafin na daliɓan da suke makarantun gwamnati ne. Idan sun haɗa da ɗalibai a makarantu masu zaman kansu a matsayin masu cin gajiyar, hakan na iya sa makarantun gwamnati su ƙara ƙara kuɗin makarantun su. Muna son ɗalibai da yawa da ke makarantun gwamnati su amfana ne.”
“Game da Iyalan da za su gajiyar abun, mun fi so ɗalibai marasa galihu da yawa su amfana da tallafin ne. Duk wanda yake samun Naira dubu ɗari biyar zuwa sama a matsayin kuɗin shiga na shekara, to zai iya ɗaukar nauyin dalibin da ke yake daukar nauyi. Ba ma son tsarin cewa sai mutum ya gabatar da ma’aikatan gwamnati biyu wadanda suka kai mataki na sha biyu zuwa sama, a matsayin wadanda suka tsaya mishi kafin ya ci gajiyar shirin. Yin haka zai saka Ɗalibai da yawa ba za su iya cika wannan sharaɗin ba. Muna son ɗalibai su nuna kawai shaidar talauci.” in ji shi.
Dangane da yadda hukumar ke son a biya waɗanda zasu ci gajiyar kuɗin, Emonefe ya ce, waɗanda ke buƙatar kuɗin makaranta za a biya makarantun su kuɗaɗen ne Kai tsaye, domin masauki, za a biya masu gidajensu, kuma masu buƙatar kuɗin aljihu za a biya kuɗin su cikin ta cikin asusunsu.