Back

Ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Tattalin Arziƙi da Zamantakewa ta baiwa Tinubu sa’o’i 48 don janye umarnin CBN kan harajin tsaron yanar gizo

Ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Tattalin Arziƙi da Zamantakewa (SERAP) ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya yi amfani da “nagartattun ofisoshinsa don gaggauta umartar Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya janye harajin da aka ɗora wa ‘yan Nijeriya na tsaron yanar gizo saboda ya saɓawa kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 [kamar yadda aka gyara] da kuma haƙƙoƙin ɗan adam na ƙasa da ƙasa.”

SERAP ta kuma buƙace shi da ya dakatar da Nuhu Ribadu da Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) daga aiwatar da sashe na 44 da sauran tanade-tanaden dokar ta tsaron yanar gizo na 2024 domin ya saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma Yarjejeniyar Haƙƙoƙin Ɗan Adam na Afrika da Yarjejeniya Ta Duniya Kan ‘Yancin Bil’adama da Siyasa.”

SERAP ta buƙace shi da “ya umurci Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, da ya gaggauta shiryawa tare da gabatar da ƙudirin gyara sashe na 44 da sauran tanade-tanaden dokar ta tsaron yanar gizo na 2024 ga Majalisar Dokokin Ƙasa domin a aiwatar da tanade-tanaden daidai da kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma haƙƙoƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa.”

A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce: “Dole ne gwamnatin Tinubu ta janye dokar CBN da ake zargin ta ɗorawa ‘yan Nijeriya harajin tsaron yanar gizo.

SERAP ta ce, “Sashe na 44(8) da ya sanya rashin biyan harajin yanar gizo daga ‘yan Nijeriya ya zama laifi, ya saɓawa kundin tsarin mulki.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?