Back

Ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Tattalin Arziƙi ta kai ƙarar Uba Sani, Wike, da sauran su kan ƙin yin bayanin bashin naira tiriliyan 5.9 da dala biliyan 4.6

Ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Tattalin Arziƙin Jama’a (SERAP) ta kai ƙarar gwamnonin Nijeriya da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike kotu “kan ƙin yin bayanin bashin naira tiriliyan 5.9 da dala biliyan 4.6 da jihohinsu da Babban Birnin Tarayya suka karɓa, da kuma buga kwafin yarjejeniyar bashin, gami da cikakkun bayanai da wuraren ayyukan da aka yi amfani da bashin.”

Ƙarar dai ta biyo bayan sanarwar da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya yi a watan jiya cewa gwamnatin da ta shuɗe ta Nasir El-Rufai ta bar bashin dala miliyan 587 da naira biliyan 85 da kuma bashin kwangila 115, wanda hakan ya sa jihar ba ta iya biyan albashi.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/592/2024 da ta shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a Babbar Kotun Tarayya a da ke Abuja, SERAP na neman kotun da ta tilasta wa gwamnonin da Mista Wike da su yi bayanin bashin naira tiriliyan 5.9 da dala biliyan 4.6 da jihohinsu da FCT suka karɓa da kuma buga kwafin yarjejeniyar bashin, da wuraren ayyukan da aka yi amfani da bashin.”

SERAP ta kuma buƙaci kotun da ta “umartar gwamnonin da kuma Mista Wike da su gayyaci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka (ICPC) domin su binciki yadda aka kashe duk bashin da jihohin su da FCT suka karɓa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?