Back

Ƙungiyoyin Ƙwadago sun rufe wasu ofisoshin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki a Nijeriya

Ƙungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC sun rufe hedikwatar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna (KEDCO) a kan ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi wa abokan ciniki na Band ‘A’.

Mambobin ƙungiyar ƙwadago ƙarƙashin jagorancin shugabannin NLC da TUC na Kaduna, Kwamared Ayuba Magaji Suleiman da Kwamared Alhassan Danfulani, sun yi kira da a gaggauta janye kuɗin wutar lantarkin.

Sun yi fatali da zargin rarrabuwar kawuna da ɓangaren wutar lantarki ke yi ta hanyar banbance ajin samar da wutar.

Hakazalika, a ranar Litinin ne Ƙungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC reshen Jihar Imo suka rufe ofishin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Enugu, (EEDC), saboda ƙarin kuɗin wutar lantarki.

Sauran waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos).

Da yake jawabi ga manema labarai a Owerri, Shugaban NLC, Kwamared Uche Chigamezu Nwigwe, ya ce dole ne su ɗauki mataki kan hukumar ta EEDC da sauran su saboda raɗaɗin da mazauna jihar ke fama da shi a halin yanzu sakamakon ƙarin kuɗin wutar lantarki.

A cewar Chigamezu, “Sama da wata guda yanzu EEDC da hukumomin gwamnati sun jefa mazauna Imo musamman ma’aikata cikin wahalhalu tare da tsawwala kuɗin wutar lantarkin da ba su yi amfani da ita ba. Sakatariyar mu ta ƙasa ta ba mu umarnin rufe dukkan ofisoshin NERC, DisCos, da EEDC da ke jihar daga yau Litinin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?