Gwamnatin Tarayya ta ce tsarin biyan bashi daga masu cin gajiyar Shirin Bayar da Bashi na Ilimi na Nijeriya (NELFund) zai fara ne shekaru biyu bayan Shirin Bautar Ƙasa (NYSC).
Sakataren Zartarwa na NELFund, Dokta Akintunde Sawyer, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a ranar Alhamis a Abuja.
Sawyer ya ce dalilin da ya sa aka ba da tsawon shekaru biyu bayan NYSC shi ne don baiwa waɗanda suka ci gajiyar damar samun isasshen lokaci don samun aikin yi da kwanciyar hankali kafin biyan.
Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta buɗe tashar NELFund ga ɗaliban da suka cancanta a watan Maris domin sannan ya buƙace su da su yi rajista domin samun kuɗaɗen.
Shugaba Bola Tinubu a ranar 12 ga watan Yuni, 2023, ya rattaba hannu kan Ƙudirin ba da Damar Samun Ilimi Mai Zurfi ya zama doka don baiwa ɗalibai marasa galihu damar samun lamuni marar ruwa don ci gaba da karatunsu a kowace manyan makarantun Nijeriya.