Manajan Daraktan Hukumar Ba Da Lamuni na Ilimi na Nijeriya (NELFUND), Mista Akintunde Sawyerr, ya bayyana cewa ɗalibai miliyan 1.2 a manyan makarantun tarayya ne za su sami lamunin ɗalibai a matakin farko.
Da yake jawabi gabanin buɗe gidan yana a ranar Juma’a, ya ce za a buɗe kashi na farko ga ɗaliban makarantun tarayya da makarantunsu suka kammala sanya bayanansu.
Yayin da yace an daidaita tsarin neman rancen ne don tabbatar da samun sauƙi ga dukkan ɗaliban da suka cancanta a manyan makarantun tarayya, ya ce masu nema za su iya fara nema daga ranar 24 ga Mayu, 2024.
A wani taron ƙarawa juna sani a ranar Litinin, ya ce rancen zai samu ga dukkan ɗaliban da ke manyan makarantun gwamnati kuma za a bayar da shi ne a matakai, inda za a fara da makarantun tarayya kafin a kai ga na jihohi.
Sawyerr ya ce wannan shiri wani muhimmin ɓangare ne na Ajandar Sabunta Fata na Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda aka tsara don ba da tallafin kuɗi (kuɗaɗe na wajibi da kuma alawus) ga ɗalibai mabuƙata, wanda zai ba su damar cimma burinsu na ilimi ba tare da matsalolin kuɗi ba.
Ya ce shirin bayar da lamuni wanda ba shi da ruwa yana da hanyoyin biya masu sassauci, wanda zai fara bayan shekaru biyu da kammala hidimar Bautar Ƙasa (NYSC), matuƙar mutum ya samu aikin yi.
Ya ce Hukumar zata biya kashi 100 na kuɗaɗen makaranta kai tsaye ga makarantu tare da ba wa ɗaliban alawus a kowane wata bisa la’akari da lokacin da makarantar take karatu.