An sako ɗan jarida na gidan talabijin na Channels, Joshua Rogers, wanda aka sace a gidansa da ke Rumuosi, yankin Obio/Akpor a Jihar Rivers.
An sake shi da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a ba tare da wani rauni ba, ƙasa da sa’o’i 24 da sace shi a ranar Alhamis.
Abokin aikinsa, Charles Oporum, ya tabbatar da labarin sakin nasa da yammacin ranar Juma’a.
“Eh, an sake shi kusan awa ɗaya da ya wuce, kuma ya sake haɗuwa da iyalinsa,” inji Oporum.
Masu gudanarwa na gidan talabijin ɗin sun kuma tabbatar da sakin Rogers a cikin wata ‘yar gajeriyar sanarwa.
Sanarwar ta ce: “An sako ɗan jarida na gidan talabijin na Channels, Joshua Rogers, wanda aka sace shi a daren jiya a Fatakwal, Jihar Ribas.
“Muna godiya ga masu kallonmu da kuma duk waɗanda suka nuna damuwarsu kan lamarin.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya kuma ga wani faifan bidiyo da ke nuna Rogers na murna da iyalansa bayan ya samu ‘yanci.
Sai dai kawo yanzu babu tabbas ko jami’an tsaro ne suka kuɓutar da shi ko kuma an biya kuɗin fansa ne domin a sake shi.
Jami’an ‘yan sanda da Jami’an Tsaro na Farin Kaya (DSS) sun ƙaddamar da aikin ceto lokacin da aka sace shi.
Rogers shine wakilin gidan talabijin na Channels a Fatakwal.