Back

Ɗan Majalisar Wakilai ya rasu

Isa Dogonyaro

Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Garki/Ɓaɓura na Jihar Jigawa a Majalisar Wakilai, Isa Dogonyaro, ya rasu.

Mohammed Bello El-Rufa’i, wanda ɗaya ne daga cikin abokan aikinsa, ya bayyana rasuwar ɗan majalisar a shafin sa na Facebook da safiyar Juma’a.

Ya rubuta: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. A yau ne muka rasa abokin aikinmu a Majalisar Wakilai, haziƙin ɗan majalisa kuma mutumin kirki. Allah SWT Ya gafarta masa, Ya sa Aljannatul Firdaus ce makomarsa”.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?