Ɗaya daga cikin ’yan sanda masu rakiya da ke cikin wani jirgin ƙasa mai zuwa Abuja ya rasa ransa a wata tafiya, da safiyar Alhamis.
Wani fasinja wanda lamarin ya faru a gaban idonsa ya ce a lokacin da jirgin ƙasan ya bar Kaduna babu wata alama da ke nuna cewa marigayin ba shi da lafiya.
Shaidan ya ce daga baya marigayin ya koka da ciwon ƙirji inda ya nemi taimako kafin ya mutu.
“Wani ɗan sanda, wanda yana ɗaya daga cikin masu rakiya a cikin jirgin Abuja zuwa Kaduna ya mutu.
Ya bar gida cikin ƙoshin lafiya. Amma daga baya a tafiyar, sai ya koka da ciwon ƙirji, ya kuma nemi abokin aikin sa ya kawo masa ruwan glucose da ruwa.”
“Babu kulawar gaggawa ta likita a cikin jirgin. Kafin likita, wanda shi ma fasinja ne, ya zo, jami’in ya riga ya mutu,” inji fasinja.
Bayan da jami’in ya mutu, an ɗauki gawarsa zuwa wani gefen jirgin, yayin da fuskarsa ke rufe.
Hotunan da aka gani sun nuna fasinjojin da suka taru suna tattaunawa kan makomar marigayin.
Jirgin ya isa Kubwa a Abuja da misalin ƙarfe 3:20 na rana daga nan ne fasinjoji suka sauka.
Jami’an tsaro da ke wurin sun hana fasinjoji ɗaukan bidiyon lamarin. Kimanin mintuna 20 da isowar jirgin, wasu motocin ‘yan sanda ne suka shiga cikin tashar domin ɗauko gawar zuwa ɗakin ajiyar gawa.