Back

Ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa ya ragu a watan Janairu – OPEC

Yawan ɗanyen mai da Najeriya ke haƙowa ya ragu kaɗan a watan Janairun shekarar nan idan aka kwatanta da yadda yake a watan sha biyu shekarar da ta gabata.

Ƙungiyar Ƙasashen Masu Arziƙin Man Fetur (OPEC) ta ce ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa ya ragu daga ganga miliyan daya da dubu dari hudu da ar’ba’in da hudu (1.422 m) a kowace rana a watan sha biyu da ya gabata zuwa ganga miliyan daya da dubu dari hudu da sha Tara (1.419m) a kowace rana a watan daya na wannan shekarar, inda ya ragu da ganga dubu uku (3000) a kowace rana, a cewar wasu majiyoyi.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin rahoton ƙungiyar OPEC na wata-wata da aka fitar a ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai rahoton ya ce man da ƙasar ke haƙowa ya tashi daga ganga miliyan daya talatin da uku (1.33) a kowace rana zuwa ganga miliyan daya da arbain da biyu (1.42) a kowace rana, bisa bayanan da aka samu a wata sadarwar kai tsaye.

OPEC ta bayyana cewa yawan ɗanyen mai ya ƙaru musamman a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Saudi Arabiya da kuma Venezuela.

Ta ƙara da cewa jimillar ɗanyen man da ake haƙowa a ƙasashen OPEC guda sha biyu ya kai ganga miliyan 26.34 a kowace rana a watan da ya gabata, wanda ya ragu da ganga 350,000 a kowace rana.

“A cewar majiyoyi na biyu, jimillar ɗanyen mai na OPEC-12 ya kai ganga miliyan 26.34 a kowace rana a watan Janairun 2024, ya ragu da ganga 350 a kowace rana, wata-wata. Yawan ɗanyen mai ya ƙaru ne musamman a ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Saudi Arabiya da Venezuela, yayin da wanda ake haƙowa a Libya, Kuwait, Iraki da Aljeriya, ya ragu,” in ji rahoton.

Dangane da samar da mai a duniya, rahoton ya ce bayanan farko sun nuna cewa yawan man da ake haƙowa a duniya a watan Janairu ya ragu da ganga miliyan 0.6 a kowace rana zuwa ganga miliyan 101.8 a kowace rana idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Man da ba na OPEC ba, gami da gas na OPEC an kiyasta ya ragu da ganga miliyan 0.2 a kowace rana, wata-wata a watan January zuwa ganga miliyan 75.5 a kowace rana. Wannan ya fi ganga miliyan 1.6 a kowace rana, shekara-shekara.

Ƙiyasin raguwar samarwa na farko a watan Janairu ya faru a cikin Amurka da sauran Eurasia kuma ƙaruwan da aka samu a China, Kanada da Brazil ne ya daidaita.

“Kason ɗanyen man da ƙungiyar OPEC ke haƙowa a duniya a watan Janairu, ya ragu da kashi 0.2 zuwa kashi 25.9 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Rahoton ya ce, “Ƙididdigan sun dogara ne kan bayanan farko na man da ba na OPEC ba, OPEC NGLS da kuma man da ba na al’ada ba, yayin da ƙiyasin samar da ɗanyen mai na OPEC ya dogara ne akan wasu majiyoyi,” in ji rahoton.

Yawan man da Najeriya ke haƙowa a halin yanzu ya yi ƙasa da harin kasafin kuɗin ƙasar na 2024 na ganga miliyan 1.78 a kowace rana.

Kasafin kuɗin Najeriya na 2024 ya dogara ne kacokan kan kuɗaɗen da ake samu daga siyar da ɗanyen mai.

A halin da ake ciki, yawan ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.418 a kowace rana a watan Disambar 2023, in ji rahoton Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arziƙin Man Fetur, OPEC, a cikin rahotonta na kasuwar mai na watan Janairu 2024, ta ce yawan ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga miliyan 100 a kowace rana, daga ganga miliyan 1.319 a kowace rana, a watan Nuwamba, a cewar wasu majiyoyin.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?