Back

[February 1, 2024]

Majalisar Wakilai ta umarci Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta mayar da N1.48bn kuɗaɗen Covid-19 a cikin kwanaki bakwai

A ranar Laraba ne kwamitin kula da asusun jama’a na Majalisar Wakilai, ya umurci hukumar kashe gobara ta tarayya da ta mayar da jimillar naira biliyan 1.48 cikin mako guda zuwa asusun tarayya, kasancewar sa kuɗaɗen shiga tsakani da ta samu na annobar COVID-19 amma wanda bata iya bada bayani akai ba.

Kwamitin da Bamidele Salam yake jagoranta ya bayar da wannan umarni ne a ranar Larabar da ta gabata biyo bayan rashin bayyanar hukumar a zaman binciken a karo na uku.

Mataimakin shugaban kwamitin, Jeremiah Umar, ya gabatar da buƙatar a maido da kuɗaɗen inda ya ce, “Sauran hukumomi da dama sun bayyana a gaban wannan kwamiti, kuma ana ci gaba da bincike. Ban ga dalilin da ya sa (sic) hukumar kashe gobara za ta yi watsi da kwamiti irin wannan ba.”

Umar ya ƙara da cewa tun da hukumar ba za ta iya bayyana a gaban ƴan majalisar ba don kawar da cece-kucen da ke tattare da kashe-kashen da aka yi na COVID-19, abin da ya dace a yi shi ne a mayar da kuɗaɗen da suka kai N1.48bn da ta tara a shekarar 2020.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da kwamitin ya yi sabbin gayyata ga wasu ma’aikatu, sashoshi, da hukumomin gwamnatin tarayya da suka saɓa da su bayyana tare da yin bayani a kan wasu tambayoyi dake kansu daga ofishin babban mai binciken kuɗi na tarayya kan biliyoyin naira da aka ware a matsayin kuɗaɗen shiga tsakani na COVID-19.

Waɗanda aka gayyata sune Ma’aikatar Noma da samar da Abinci ta Tarayya-N50.5 bn, Ofishin Akanta Janar na Tarayya-N33bn, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya, ta hanyar Cibiyar Raya Mata ta Ƙasa-miliyan N625, Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Ƙasa-N25bn, da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya-N10bn.

A nasa jawabin, Salam ya koka da yadda hukumar kashe gobara ta tarayya ta yi watsi da sammacin kwamitin sau uku yayin da sauran MDAs suka yi haka sau biyu kowanne, yana mai cewa an baiwa hukumar mako guda ta bayyana, ko kuma ta fuskanci takunkumi.

Ya ce, “Ma’aikacin gwamnati da ya kasa amsa tambayar babban mai binciken kudi a cikin kwanaki 21 na rashin karɓar kuɗaɗen shiga na gwamnati, za a ƙara masa kuɗi sannan a tura shi wani jadawalin. Inda jami’i ya kasa bayar da gamsasshiyar amsa ga tambayar tantancewa cikin kwanaki bakwai saboda gazawarsa ta bada bayani akan kuɗaɗen shiga na gwamnati, za a ƙara wa wannan jami’in ƙarin ƙudin da abin ya shafa sannan a miƙa su ga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ko kuma hukumar kula da laifuka mai zaman kanta da hukumar kula da sauran laifuka da ke da alaka.

“Wannan kwamitin yana da ayyuka da yawa a gabansa. Binciken COVID-19 ɗaya ne kawai daga ciki; dole ne mu matsa zuwa wasu ayyuka,” in ji shi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?