Back

Abin da ya sa ba zan sasanta da ‘yan bindiga ba, inji Gwamna Radda

Gwamna Dikko Umaru Radda

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya ce ba zai sasanta da ‘yan bindiga ba saboda ba ya son su ji gwamnati baza ta iya komai ba.

Radda wanda ya kuma bayar da shawarar ‘yan sandan jihohi a wani mataki na magance matsalar rashin tsaro da ya addabi jihohi ciki har da Katsina, ya ce akwai buƙatar gwamnoni su riƙa kula da harkokin tsaro a jihohinsu.

Radda ya ce a tsarin da tsarin mulki ya tanada a halin yanzu, gwamnonin suna ganin kamar ba su da wani tasiri a harkar tsaro a jihohinsu domin duk hukumomin tsaro na al’ada suna amsawa ga shugabanninsu, sai dai idan aka yi sabbin tsare-tsare, kamar ƙungiyar Katsina Community Watch Corps da ke taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro.

“Wasu mutane na cewa hanya ɗaya tilo da za a magance wannan matsalar ita ce ta hanyar tattaunawa. Na shaida wa Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) cewa a Katsina, ba zan yi sulhu da ‘yan bindiga ba, domin mun yi shi a gwamnatin da ta shuɗe kuma hakan bai haifar da sakamako mai kyau ba.

“Mun ba su kuɗaɗen masu biyan haraji amma suka samarwa kansu kayan aiki, suka sami ƙarin makamai tare da sake kai hare-hare kan ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa “Mutane sun zaɓe mu ne saboda mun yi musu alƙawarin za mu kawo zaman lafiya da tsaro kuma idan babu zaman lafiya ba za a iya cimma komai ba. Yana da matuƙar ban takaici idan ka je waɗannan al’ummomin da abin ya shafa, ka ga halin da makarantunsu da asibitocin su ke ciki, wasu daga cikinsu sun zama sansanin ‘yan bindiga. Shin a hakan zamu ci gaba?

“Ba za mu naɗe hannayenmu ba yayin da wasu ke kashe mutane, suna lalata da kuma yi wa mutanenmu fyaɗe, saboda ba mu ke da iko kan tsaro. Don haka, mun yanke shawarar cewa dole ne mu sami wasu hanyoyi a matsayinmu na shugabanni don kare mutanenmu.

“Hanyata ta farko wajen tunkarar wannan matsala ita ce, na yanke shawarar cewa ba zan tattauna da duk wani ɗan bindiga ba, domin hakan zai sa su ji cewa ba mu da yadda zamu yi kuma dole ne mu bi ƙa’idojinsu.

Radda ya ce shawarar da ya yanke na kafa ƙungiyar sa ido ta al’umma yana samun sakamako yayin da aka mayar da ‘yan bindigar zuwa gaɓar dajin. Gwamnan ya ce abin takaici ne, idan aka ji wasu bayanai na cewa tsarin yin amfani da ’yan ƙasar da aka horar da su wajen kara wa ƙoƙarin jami’an tsaro ba daidai ba ne, yana mai cewa masu irin wannan ra’ayi ko dai sun jahilci abubuwan da ke faruwa a jihar ko kuma sun kasance masu ƙeta ne kawai.

“Lokacin da muke son ɗaukar ma’aikatan ƙungiyar Katsina Community Watch, ba mu ba ta tsarin ‘Yan Sakai’ ko kuma na ‘yan banga ba. Hukumomin tsaro na al’ada sun ɗauke su aiki tare da horar da su ta hanyar da ta dace. An horar da su kan yaƙi, sarrafa makamai da kowane ɓangare na horon tsaro kuma suna da ƙwarewa sosai.”

“Shawara ce mai kyau, kuma dokar da Majalisar Dokokin jiharmu ta amince da ita kuma mazajen suna aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro na yau da kullun,” inji shi.

Sai dai ya yi kira da a samar da tsarin da ya dace a yankin domin tunkarar matsalar rashin tsaro saboda yawancin jihohin yankin Arewa maso Yamma na fama da fashi da garkuwa da mutane.

Gwamnan ya ce da jami’an tsaro na jihar, gwamnatinsa ta samu nasarar sauya guguwar ‘yan bindigan da har zuwa yanzu ke tunkarar babban birnin Katsina, amma yanzu an mayar da su ƙananan hukumomin da ke kan gaɓa, wanda ya zama fagen daga.

Ya ce ‘yan ta’addan da suka sake kunno kai a baya-bayan nan ba komai ba ne illa nuna takaici da ‘yan ta’addan suka yi domin an mayar da su baya, inda ya ce a dalilin haka ne suka kai hari ƙauyuka tare da ƙona gidaje.

Gwamnan ya ce hakan ba zai sa gwamnatin sa ta yi ƙasa a gwiwa ba domin za ta ci gaba da ingizawa har sai an murƙushe ‘yan bindigan.

Gwamna Radda ya ce wani labari na yaudara shi ne, wai a batun ‘yan bindiga, Fulani ne ke adawa da Hausawa, inda ya bayyana cewa wannan ba gaskiya ba ne, kuma karkatar da hankali ne.

“Ku shiga cikin Katsina yanzu a gwada banbance wanene Bahaushe da wane Bafulatani. Ba za ku iya yin hakan kawai ba. Mu duka mutane ɗaya ne. Ni Bafulatani ne daga iyaye biyu. Amma ‘yan bindigar masu laifi ne kawai kuma dole ne mu ɗauke su haka,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?