Back

Abubuwa goma sha biyu da ya kamata ku sani game da marigayi Herbert Wigwe, wanda ya kafa bankin Access

Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Access Holdings Plc, Herbert Wigwe, ya rasu.

Ana tunanin Wigwe ya mutu ranar Juma’a a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar California ta Amurka.

Ga abubuwa goma sha biyu da ya kamata ku sani game da shi:

1. An haifi Herbert Wigwe a ranar sha biyar ga watan bakwai na shekarar alif dari tara da sittin da shida, (15, August, 1966). 

 2. Ya rasu yana da shekaru 58. 

3. Ya yi Digiri a fannin lissafi (Accountancy) a Jami’ar Najeriya ta Nsukka, Jihar Enugu.

4. Yayi babban digiri (MA) a fannin Banki da hada-hadar Kuɗaɗe daga Jami’ar North Wales ( College of North Wales), da Kuma wani babban digirin na kididdiga (MSc) a fannin tattalin arziƙi daga Jami’ar London.

5. Wigwe ya fara aikin sa ne a Coopers & Lybrand, a Jihar Legas, a matsayin mai ba da shawara kan harkokin gudanarwa, inda daga baya ya samu cancantar zama akanta.

6. Bayan ya yi aiki a Capital Bank, ya koma Guaranty Trust Bank (GTB) inda ya kwashe sama da shekaru goma yana hada-hadar banki na kamfanoni da hukumomi inda ya zama babban darakta mai kula da harkokin banki na hukumomin.

7. Wigwe ya taɓa zama Shugaban Bankin Access Ghana Limited, Access Investment & Securities Limited, Central Securities and Clearing System (CSCS). Ya kasance Shugaban Bankin Access (UK) Limited har zuwa rasuwarsa.

8. ƙungiyar Boys’ Brigade (BB), a shekara ta dubu biyu da sha shida (2016), ta ƙaddamar da Herbert Wigwe a matsayin Majibincin Jiha ga Majalisar Jihar Legas, domin karrama shi kan “ayyukan shi na tallfawa a cikin al’umma da kuma gudunmawar ci gaban matasa”, 

9. Wigwe ya samu kyautar Gwarzon Bankin Shekara ta dubu biyu da sha shida (2016), ta jaridun The Sun da kuma ta Vanguard.

10. A cikin 2016, Wigwe ya kafa “The HOW Foundation”, wata ƙungiya mai zaman kanta domin bayar da tallafi.

11. A watan goma na shekarar alif dubu biyu da ashirin (2022), Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ba shi lambar yabo ta ƙasa ta Najeriya mai suna Kwamandan Hukumar Neja (CON).

12. Marigayin yana da hannu a ginin Jami’ar Wigwe da ke Isiokpo, Jihar Ribas. Ana sa ran jami’ar za ta fara aiki a watan tara na wannan shekarar (2024).

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?