Back

Afenifere ga Tinubu: Ba ka da uzuri na ƙin sauya fasalin Nijeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta shaida wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa ba shi da wani uzuri na ƙin sake fasalin Nijeriya kasancewar an zaɓe shi a bisa dandamali da aƙidar ƙungiyar.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ta kammala tsarin ta na sauya fasalin ƙasar nan.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ta yi tsarin sake fasalin a kan amfani da tsarin majalisa irin wanda aka yi a zamanin Tafawa-Ɓalewa a Nijeriya.

Sakataren Yaɗa Labarai na Afenifere, Mogaji Gboyega Adejumo, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron shugabannin ƙungiyar da aka gudanar a Isanya Ogbo Ijebu da ke Jihar Ogun a gidan Pa Ayo Adebanjo, shugaban Afenifere.

Taron, wanda Adebanjo ya jagoranta, ya samu halartar Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Oba Oladipo Olaitan; Ma’ajin Kuɗi, Cif Supo Sonibare; tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Legas, Cif Misis Kofoworola Bucknor; Prince Justice Faloye; Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Cif Segun Ojo, Bashorun Segun Sanni, da sauran su.

Afenifere wacce ke ɗaya daga cikin masu fafutikar kawo sauyi a Nijeriya, ta kafa wani kwamiti da zai tattara ra’ayoyin masu ruwa da tsaki kan wannan buƙata.

A taron ƙungiyar da aka gudanar a ranar Talata, kwamitin ya miƙa rahoton sa.

Adejumo ya ce ƙungiyar ta ɓullo da tsarin sauya fasalin ƙasar nan inda ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta yi amfani da tsarin.

Ƙungiyar ta ce Tinubu kafin zaɓen sa yana kan gaba wajen kiran a sake fasalin ƙasar nan, don haka bai kamata ya “ci amanar” ‘yan Nijeriya ba.

Afenifere ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya ci gajiyar kiran a sake fasalin.

Ta ce, “Wani lokaci a shekarar da ta gabata a watan Nuwamba, an kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Oba Oladipo Olaitan don tattara ra’ayin Afenifere kan sake fasalin, kuma a yanzu kwamitin ya ce an kammala rahoton.

“Duk da haka, wannan rahoto har yanzu shugabannin ƙungiyar za su yi nazarin shi, daga nan ne za a kai shi babban taro inda dukkanin ‘yan ƙungiyar za su san matsayar mu kan sake fasalin ƙasa a matsayin mu na Afenifere sannan za mu buga rahoton, mu yi namu tallace-tallacen daban-daban a kai don mutane su san abin da muka yi imani da shi game da sake fasalin ƙasar.

“Shi kan sa Tinubu ɗan Afenifere ne, an zaɓe shi a kan dandamali da aƙidar Afenifere. Ya taɓa maka Gwamnatin Tarayya a kotu a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo har sau 31 don a sake fasalin ƙasar.

“Bai yi wani abu ba a lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Buhari ya yi shekara takwas, wataƙila domin ya san cewa ‘yan Arewa ba za su aiwatar da sauya fasalin ba saboda suna ganin hakan ba zai amfane su ba.

“Amma Tinubu yana nan a matsayin sa na Shugaban Ƙasa, yana da alhaƙin amsa mana duka a matsayin ɗan Afenifere, kuma abin da duk Yarbawa suka yi a ƙarƙashin ƙungiyar Afenifere a Adamasingba, Ibadan, Jihar Oyo, a 2017, ba abin da muke so illa a sake fasalin.

“A wannan taron na 2017, mun gayyaci Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da Yankin Tsakiya kuma wannan shi ne farkon abin da muke kira Dandalin Shugabannin Kudu da Yankin Tsakiya.

“Don haka har yanzu muna taro a wannan dandalin yayin da sauran shiyyoyin su ma za su gabatar da shawarwarin su.

“Don haka abin da muka ɗauka zuwa tattaunawar 2014 shi ne abin da muke ƙaddamarwa duk da cewa wasu abubuwa sun canza. Sannan za mu gabatar da shi gaban Majalisar Dokoki domin amincewarsu.”

Da aka nemi ya ba da haske kan rahoton na Afenifere, sai Adejumo ya ce, “Abin da muke gabatarwa shi ne tsarin gwamnati na falimantare. Marigayi Cif Obafemi Awolowo ba sai ya yi yaƙin neman zaɓe a Ijebu Igbo ba, abin da kawai zai yi shi ne ya yi nasara a Ikenne ya zama ɗan majalisa kuma duk wanda ke shugabantar jam’iyyar ya zama Firayim Minista ko Firimiya.

“Tsohon Lardin Yamma daga Badagry ne a Legas zuwa Asaba a Jihar Delta a yau amma bai taɓa yin kamfen a ko’ina ba kamar yadda muke yi a yanzu.

“(Tsarin) yana sa a riƙa gudanar da gwamnati cikin arha, babu wanda zai sake kashe biliyoyi kan kamfen.

“Za a buƙaci kusan naira miliyan 100 ne don yaƙin neman zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi.

“Don haka, a wannan tsarin ne za ku shigo majalisa daga mazaɓar ku, daga nan ne za ku zaɓi ministocin ku da kwamishinonin ku, ba za a sake naɗa wani daga waje ba sai waɗanda aka zaɓa a majalisar.

“Da wannan tsarin na gwamnati, za mu kashe kashi ɗaya bisa goma na kayan aikin da muke amfani da su wajen tafiyar da wannan tsarin mulkin shugaban ƙasa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?