Hukumar ta sanya farashin ƙarshe naira 6,617,032.91 ga tsohon masu biya, sabuwar rijista kuma naira 8,254,464.74
Za a biya naira 8,225,464.74 na duk wani sabon rajista na aikin hajjin 2024 daga maniyyatan Arewa da kuma naira 8,454,464.73 daga Kudu, kamar yadda lambobin da hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta fitar ranar Lahadi.
A cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta rabawa manema labarai, ta bayyana yadda hargitsi a kasuwar canji ya shafi matakin.
Cikakken bayanin shi ne kamar haka:
Hukumar Alhazai ta Nijeriya, NAHCON, ta yaba da irin fahimta da damuwa da aka nuna mata a bainar jama’a da kuma a keɓance kan matsalar Hajjin 2024 da ta tsunduma cikin ta. Wannan nuna goyon baya ya baiwa hukumar fatan masu ruwa da tsaki za su yi komai domin samun nasarar aikin Hajji mai zuwa. A halin da ake ciki, Hukumar ta ga ya zama wajibi ta yi ƙarin haske game da shirye-shiryen kuɗin Hajji na shekarar 2024.
An yarda cewa shirye-shiryen aikin Hajji yana bin jadawali mai tsauri. Dangane da aikin Hajjin 2024 kuwa, jadawalin shirye-shiryen da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar ya fara da wuri ba kamar yadda aka saba ba kuma ana sa ran kammala shi kafin lokacin da aka saba. NAHCON ta yi yunƙurin bin tsarin da ma’aikatar ta zayyana.
Sai dai kuma rashin biya da lattin biya kuɗin aikin Hajji na waɗanda abin ya shafa ya sa ya zama dole a yi gyare-gyare, wanda hakan ya sa aka sauya ranakun kwanaki biyu, inda ranar 12 ga watan Fabrairun 2024 ya zama na ƙarshe. Waɗannan sauye-sauyen, abin takaici, sun sa wa’adin tattara kuɗin Hajji ya ragu bayan daidaita farashin kuɗaɗen ƙasashen waje, lamarin da ya haifar da wani sabon ƙalubale.
Abin da ake nufi da daidaitawa a cikin lissafin kuɗin aikin Hajji shi ne, ta fuskar ƙalubalen kuɗi na duniya, tare da sabon tsarin canjin kuɗi, a yanzu maniyyatan Nijeriya za su fuskanci ƙarin kuɗin aikin Hajji da ba a yi tsammani ba, duk da cewa sun riga sun biya ƙayyadadden farashin kuɗin aikin Hajji na kusan naira miliyan 4.9, ya danganta da yankin tashi kamar yadda gwamnati ta amince.
Gwamnatin Tarayya ta ga hikimar sa baki a madadin maniyyatan Nijeriya ta hanyar dabaru daban-daban da suka haɗa da rage farashin. Abin takaici, shisshigin sun kasa cika adadin da suka cika wa’adin rajista na ƙarshe. Wannan ya sanya Hukumar cikin ruɗani. Babban abin da ya fi muni shi ne, a yanzu kimanin alhazai 50,000 ne suka biya kudin Hajji da aka sanar zuwa yanzu na kimanin naira miliyan 4.9 kuma a halin yanzu kuɗaɗen nasu na hannun Hukumar.
Bisa la’akari da gaggawar lamarin, ya zama dole hukumar NAHCON ta duba wasu zaɓuɓɓuka, ciki har da ƙarfafa gwiwar Gwamnatocin Jihohi da masu hannu da shuni da su sa baki a madadin alhazai. Wannan damar har yanzu tana buɗe. Hakan zai cika tsoma bakin Gwamnatin Tarayya da ta yi ƙoƙarin tallafa wa alhazan Nijeriya Musulmi wajen sauke nauyin da aka ɗora musu na addini. Abin yabawa ne, manufar gwamnati ta mayar da hankali wajen rage farashin canji ya ƙara rage farashin Hajji.
Labari mai daɗi yanzu shine yadda naira ta ƙara daraja zuwa naira 1,474.00 akan dala a satin da ya gabata kuma bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki, tare da fatan NAHCON ta tabbatar da ganin Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin daidai wa daida ga ɗaukacin maniyyatan da suka rigaya suka yi rajista waɗanda aka karɓa kuɗaɗensu, Hukumar ta yanke shawarar cewa kowane mahajjaci zai biya cikon naira 1,918,032.91 daidai da kuɗin waje na yanzu.
Ana shawartan maniyyatan da har yanzu suke son shiga aikin Hajji na 2024 ta wannan sanarwar da su biya naira 1,918,032.91 da kafin ƙarfe 11:59 na dare na 28 ga Maris 2024.
Hukumar za ta kashe na’urar ta nan da ranar 29 ga Maris, kuma babu wani biya za a karɓa bayan nan.
Ana shawartan alhazan da abin ya shafa da su ziyarci hukumar alhazai ta jiha domin tabbatar da matsayinsu. A ƙasa akwai jadawalin adadin maniyyatan da suka biya kuɗin aikin Hajji bisa ga jihohi kuma su ne adadin da ake sa ran za su ci gajiyar tallafin:
JAHOHI DA ADADIN KUJERU DA AKA BIYA:
1 ABIYA
2 ADAMAWA
1,767
3 A/IBOM
4 ANAMBRA
5 BAUCHI 2,290
6 BAYELSA 13
7 BENUE 87
8 BORNO 1,780
9 C/RIVER 0
10 DELTA 40
11 EBONYI 13
12 EDO 265
13 EKITI 186
14 ENUGU 18
15 FCT,ABUJA 2,489
16 GOMBE 1,262
17 IMO 98
18 JIGAWA 1,260
19 KADUNA 4,656
20 KANO 2,906
21 KATSINA 2,654
22 KEBBI 3,344
23 KOGI 13
24 KWARA 3,100
25 LAGOS 1,857
26 NASARAWA 1,866
27 NIGER 3,200
28 OGUN 925
29 ONDO 491
30 OSUN 1,548
31 OYO 1,047
32 PLATEAU 1,345
33 RIVERS 42
34 SOKOTO 3,563
35 TARABA 1,000
36 YOBE 1,290
37 ZAMFARA 1,596
38 SOJOJI 403
JIMILLA = 48,414
Sai dai za a biya cikkaken kuɗi naira 8,225,464.74 na duk wata sabuwar rijistar aikin hajjin 2024 daga yau 24 ga watan Maris daga yankin Adamawa/Borno. Daga shiyyar Arewa, sabbin masu biya za su biya naira 8, 254,464.74 yayin da sabon biyan daga shiyyar Kudu zai kasance naira 8,454,464.74 a matsayin kuɗin aikin Hajji. Duk nau’ikan za a biya a cikin wa’adin ƙarshe.
A yayin da hukumar ta yi nadamar wannan gajeriyar sanarwar, ya zama babu makawa saboda tsananin gargaɗin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta yi wa Nijeriya dangane da tsaikon da aka samu wajen bin tsarin aikin Hajji.
A baya dai hukumar ta NAHCON ta nemi a ƙara wa hukumar lokaci ba tare da son rai ba, kuma a yanzu haƙurin Ma’aikatar yana raguwa.
Dangane da masu son janye rajistar aikin Hajjin 2024, ana shawartan su da su nemi a mayar musu da kuɗaɗen daga jihohinsu a hukumance wanda za a kula da su da muhimmanci.
Kwanaki huɗu masu zuwa na da maatuƙar muhimmanci ga masu ruwa da tsaki, musamman masu son shiga tsakani don tallafawa alhazansu, domin ɗaukar matakan da suka dace da kuma tabbatar da shirye-shiryen aikin Hajji cikin sauƙi.
Hukumar NAHCON ta ci gaba da jajircewa wajen sauƙaƙawa musulman Nijeriya aikin hajji da kuma neman haɗin kai daga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.