Back

Air Peace ya fara tafiye-tafiye daga Legas zuwa Landan kai tsaye

A ranar Asabar ne kamfanin Air Peace ya fara tafiye-tafiye daga Legas zuwa Landan.

Tun da farko kamfanin jirgin ya bayyana shirin fara gudanar da tafiye-tafiyen jiragen sama kai tsaye zuwa Landan a ranar 30 ga Maris yayin wani taron share fage da kamfanin ya shirya a watan Fabrairu.

A watan Nuwamba, Shugaban Kamfanin Air Peace, kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Allen Onyema, ya sanar da cewa, kamfanin ya samu nasarar samun Izinin Jigila na Ƙasashen Waje da kuma Izinin Gudanar da Ayyuka na Ƙasa ta Uku.

Bayan haka, kamfanin jirgin ya cancanci yin tafiye-tafiye zuwa Turai da Ingila.

Kamfanin jirgin ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Kamfanin jirgin ya rubuta a shafin X, “Sabis na Landan ya fara kuma muna farin cikin sake samun wani nasara a cikin tafiyarmu na ci gaba da samar da haɗin kai a birane.

“Babban godiya ga duk wanda ya ba da gudummawar nasarar wannan ƙaddamarwa.”

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci Gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo; Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anita, da dai sauran su, sun halarci tashin jirgin na farko zuwa Landan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?