Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya gayyaci Babban Alƙalin Babbar Kotun Tarayya, da kuma Babbar Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kano bisa wasu hukumce-hukumce na wucin gadi da suka ci karo da juna dangane da Masarautar Kano, lamarin da ya haifar da rashin tabbas a jihar.
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin Mai Shari’a S. A. Amobeda, ta bayar da umarnin korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga Fadar Ƙofar Kudu, tare da ƙarfafa ikon Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
“An ba da umarnin wucin gadi da ke hana waɗanda ake ƙara gayyata, kamawa, tsarewa, barazana, tsoratarwa, musgunawa mai ƙara, ko tauye haƙƙinsa,” inji Mai Shari’a Amobeda.
Ya ƙara da cewa, “Wannan umarni ya tabbatar da cewa Sarki Aminu Bayero ya samu duk wani haƙƙi da gata da aka same shi ta hanyar matsayinsa.”
A ɗaya hannun kuma, Babbar Kotun Jihar Kano a ƙarƙashin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kare Sarki Muhammadu Sunusi da sauran manyan mutane daga cin zarafin da hukumomin jihar ke yi musu. Wannan odar ta hana duk wani tsangwama ga ‘yancin cin gashin kan Sarki da kuma ƙwace manyan alamomin ikonsa, kamar tagwayen mashi, Hular Sarauta ta Dabo, da takalman gashin jimina.
Mai Shari’a Amina ta jaddada cewa, “An ba da umarnin na wucin gadi da zai hana waɗanda ake ƙara takurawa ko tsoratar da masu ƙara ko kuma ƙwace duk wata alama ta ikon Sarki.”
Ta ƙara da cewa, “An umurci waɗanda ake ƙara da su ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da kuma yanke hukunci.”
Waɗannan umarni da suka ci karo da juna sun haifar da ruɗani mai yawa dangane da iko da kariyar sarakunan a Kano.
A ranar 13 ga watan Yuni ne za a ci gaba da sauraren ƙarar Babbar Kotun Jihar, yayin da Babbar Kotun Tarayya ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 4 ga watan Yuni.