Dalilin da yasa muke neman sabon mafi karancin albashi naira N1m – Ajaero

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana cewa bukatar ta na tsarin sabon albashi na iya karuwa zuwa Naira miliyan daya a kowanne wata idan har tabarbarewar tattalin arzikin kasar ya ci gaba.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, ya bayyana karuwar hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar naira a matsayin manyan abubuwan da suka kara neman bukatar hakan.
Ajaero ya ce: “Wannan Naira miliyan dayan na iya zama mara amfani idan faduwar darajar Naira ya ci gaba, idan hauhawar farashin kayayyaki ya ci gaba da raguwa. Bukatar Ma’aikata daidai take da abin da ke faruwa a cikin al’umma.
“Za ku tuna cewa a lokacin da muke tunanin Naira 200,000, farashin canji ya kai N900. Kamar yadda muke magana a yau Kuma, farashin canjin dala ya kai kusan N1,400 ko ma fiye da haka.
“Waɗannan su ne batutuwan da ke ƙayyade buƙatu kuma hakan yana shafar tsadar rayuwa kuma a koyaushe muna faɗin cewa buƙatarmu za ta dogara ne akan kimar darajar rayuwa.
“Za ku yarda da ni cewa buhun shinkafa ya kai kusan N60,000 zuwa N70,000. Kayayyakin abinci suna kurewa. Yanzu, mafi ƙarancin albashin ba zai isar da ma’aikaci sufurin zuwa wurin aiki ba ko da na mako ɗaya?
“Dole ne mu sanya hannu a cikin duk waɗannan batutuwa. Kuma hakan ne zai tabbatar da kudurin gwamnatin tarayya na yin wannan tattaunawar,” inji shi.
A yau ne gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago, NLC, da TUC, za su hadu domin yin muhawara kan matakan da suka dauka dangane da gargadin yajin aikin na kwanaki 14.
Kungiyoyin dai na zargin gwamnatin Najeriya rashin cika yarjejeniyar da suka kulla a baya wadanda suka hada da bayar da albashin ma’aikata na wucin gadi.
Ya ce: “wata daya kacal daga cikin Naira 35,000 aka biya ma’aikatan gwamnati.
Haka kuma, babu wata shaida ta biyan duk wani ma’aikacin dubu ashirin da biyar a matsayin tallafi. Irin abin da ya haifar da abin da ke faruwa a ma’aikatar jin kai ke nan.
“Babu wani manomi kuma da ya zo ya shaida mana cewa an ba shi taki daga wannan gwamnatin. Ban sani ba ko takin na sayarwa ne, ko kuma na manoma ne,” inji shi.