
Ali Nuhu (hagu) yayin bikin miƙa ragamar mulkin
A ranar Talata ne sabon Manajan Darakta na Hukumar Fina-Finai ta Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu, ya fara aiki a hukumance tare da yin alƙawarin gaggauta bunƙasar masana’antar shirya fina-finan Nijeriya da himma da jajircewa.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Mista Brian Etuk, ya bayyana cewa a wajen taron miƙa ragamar mulki da aka yi a hedikwatar Hukumar NFC da ke Jos, Jihar Filato, Nuhu ya ce ya ƙuduri aniyar yin amfani da ɗimbin gogewar da ya samu wajen cigaban masana’antar fina-finan Nijeriya.
Nuhu, sabon shugaban NFC kuma na bakwai, ya jaddada fatan Gwamnatin Tarayya, na fina-finai da sauran masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar Nijeriya kan rawar da ya kamata hukumar ta taka a fannin ƙirƙire-ƙirƙire na ƙasa da ma duniya baki ɗaya.
Ya kuma ba da tabbacin cewa duk da irin nauyin da ake da shi, ya ƙuduri aniyar tafiyar da NFC zuwa ga mafi kyawun da ba a taɓa ganin irinsa ba a cikin isar da aiki wanda zai kasance akan lokaci, mai amfani, mai ɗorewa, kuma mai tasiri.
Ya ce aikin yin amfani da damar da ɓangaren ƙirƙire-ƙirƙire na Nijeriya ke da shi, musamman ɓangaren shirya fina-finai, don ciyar da manufofi da tsarin Gwamnatin Tarayya gaba wajen bunƙasa ci gaban ƙasa, zai kasance ne a kan turbar da ke cikin kundin tsarin hidima na NFC.
Nuhu ya lissafo tsarawa da aiwatar da ingantattun manufofi da tsare-tsaren masana’antar fim; haɓaka horo da shirye-shiryen haɓaka iyawa don haɓaka hazaƙa da inganta ƙwarewa; haɓaka abubuwan samar da fina-finai don haɓaka ci gaba da gasa a masana’antu; ganin fina-finan Nijeriya a cikin ƙasar da kuma ƙasashen waje; haɗin gwiwa tare da manyan hukumomi da ƙungiyoyi na jama’a da masu zaman kansu, da masu ruwa da tsaki na duniya – don haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire, jawo hannun jari, da samar da ayyukan haɗin gwiwar fina-finai.
Ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa naɗin nasa, kamar yadda ya yaba kuma ya kuma yi alƙawarin tallafawa manufofin Barista Hannatu Musawa, Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arziƙin Ƙirƙire-ƙirƙire, wajen bunƙasa fannin fina-finai.
Da yake jawabi tun da farko, Mista Edmund Peters, Daraktan NFC, na Aikin Tallafawa Ayyuka da Masana’antu, ya bayyana cewa, kamfanin ya samu gagarumar nasarori tun lokacin da aka kafa shi a shekarar 1979.
Ya bayyana ƙwarin guiwar masu gudanarwa da ma’aikata kan yadda Nuhu zai iya jagorantar kamfanin zuwa wani matsayi mai girma.
Peters ya ce sabon babban jami’in “ya samu damar gadon ma’aikata masu ƙwazo waɗanda a shirye suke su ba ku goyon baya yayin da kuka fara wannan sabuwar tafiya” na yin amfani da ƙarfin da NFC ke da shi na yin aiki don bunƙasa harkar fim gaba ɗaya.
Taron dai ya samu halartan masu ruwa da tsaki a harkar fim da masu gudanarwa da ma’aikatan NFC da kuma manyan jami’an gwamnati.
Manyan baƙi da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Abba El-Mustapha, Babban Sakataren Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano; Barista Ezra Jinang, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Filato, kan Ƙirƙire-Ƙirƙire da Nishaɗi; Alhaji Sani Muazu, fitaccen jarumin Kannywood; Sir Eward Fom na Ƙungiyar Masu Shirya Fim (AMP); Alfred Mgbejume, Achor Yusuf, da Umar Tanko Ravi, wakilan shugabannin Ƙungiyar ‘Yan wasan kwaikwayo ta Nijeriya (AGN), Ƙungiyar Daraktoci ta Nijeriya (DGN), da Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN), bi da bi, da ’yan fim da dama.