Back

Allah ne ya ƙaddara dawowata, inji Sarki Sanusi

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana mayar da shi kan muƙaminsa a matsayin nufin Allah.

An dawo da Sanusi ne ranar Alhamis kuma ya karɓi takardar naɗin nasa kwana guda bayan da Gwamna Abba Yusuf ya rattaba hannu a kan Dokar Masarautar Kano ta shekarar 2024.

Hakan ya sa aka mayar da shi bakin aiki shekaru huɗu bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya tsige shi.

A wani taron karɓar takardar naɗin daga Gwamna Yusuf, Sarki Sanusi ya ce Allah ne ya mai da shi kan muƙaminsa.

“Larabawa sun kasance suna cewa a cikin duk abin da muka shaida akwai darasi da ke nuna mana cewa Allah yana nan. Duk abin da ya faru da mutum Allah ne ya ƙaddara, kuma ga masu hankali, darasi ne. Allah ɗaya ne, kuma duk abin da ya yi, babu mai iya canzawa, kuma abin da bai yi ba, ba wanda zai iya,” inji shi a Gidan Gwamnati da ke Kano a ranar Juma’a bayan ya karɓi takardar naɗin nasa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?