Back

Al’ummar Fulani sun zargi sojoji da ƙona gidaje da kashe shanu a Filato

A jiya ne al’ummar garin Luggere da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato, ta zargi jami’an ‘Operation Safe Haven,’ masu wanzar da zaman lafiya a yankin da ƙona musu gidaje da motoci da sauran kadarori.

Al’ummar ta kuma zargi jami’an tsaro da buɗe musu wuta a kan shanunsu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu, inda suka kuma ce sun lalata duk wasu muhimman kayayyaki na al’ummar ciki har da rijiyar burtsatse.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da tsakar dare a lokacin da suke barci biyo bayan kisan da aka yi wa wani soja a wurin haƙar ma’adinai a unguwar Shurun ​​da ke gundumar Ropp a ƙaramar hukumar Barkin Ladi.

Al’ummar ta yi zargin cewa sojoji sun fara harbe-harbe ta sama kafin su ƙona gidajensu da sauran kayayyakinsu, inda ta ƙara da cewa da yawa daga cikinsu sun gudu daga cikin al’ummar, yayin da sojojin suka kama wasu tare da tara su a cikin motoci.

Bala Salihu, wani mazaunin unguwar da aka ƙona gidansa ya ce, “Muna cikin barci ne sojoji suka isa unguwar. Sun ƙona gidaje da ababen hawanmu saboda laifin da ba mu aikata ba.

“Wurin haƙar ma’adinai da aka kashe sojan ya yi nisa da al’ummarmu. Akwai ma al’ummomi biyu kusa da wurin haƙar ma’adinai kafin namu. Babu wata shaida da ke nuna cewa wanda ya kashe sojan ya fito daga yankinmu.

“Ba mu taɓa fuskantar irin wannan ta’asa ba a baya. A farkon watan nan an kashe mana shanu, yanzu haka an ƙona mana gidaje da dukiyoyinmu. Lokacin da aka kashe shanun mu sama da 100, jami’an tsaro sun roƙe mu da mu yi haƙuri. Me jami’an tsaro suke so mu yi? Ba a gudanar da bincike ba kafin matakin nasu.”

Uthman Abdullahi, wani mazaunin yankin ya ce sun yi asarar miliyoyin nairori a lokacin farmakin, kuma ya yi kira da a gudanar da bincike.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom, da aka tuntuɓe shi kan lamarin, ya yi alƙawarin gudanar da bincike kan lamarin tare da bayar da rahoto.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?