Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, ya shawarci al’ummar Kano da su yi watsi da labaran ƙarya da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na cewa Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Juma’a a Babban Masallacin Ƙofar Kudu dake Kano.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.
Kwamishinan ya kuma bayar da tabbacin cewa, an gudanar da dukkan shirye-shiryen tsaro domin Alhaji Aminu Bayero ya gudanar da Sallar Juma’a a Masallacin Fadar Nasarawa da yake zaune.
CP ya kuma bayar da tabbacin cewa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro na jihar za su samar da ingantaccen tsaro a fadar da ake sa ran Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi sallar Juma’a.
“Don haka an shawarci jama’a da su yi watsi da rahotannin ƙarya da bayanan ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta, su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da fargabar zagi ko tsoratarwa ba tare da tabbatar da cewa ‘yan sanda za su ci gaba da samar da tsaro da ya dace domin tabbatar da cewa mazauna yankin sun gudanar da sallarsu ta Juma’a cikin aminci ba tare da barazana ga rayukansu da dukiyoyinsu ba”.