Back

An Buƙaci Alhazan Kaduna Su Cika Kuɗin Aikin Hajji Nan Da 12 Ga Fabrairu

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta shawarci alhazai masu niyyar zuwa aikin Hajji da su kammala biyan kuɗaɗen da suka biya na aikin Hajji nan da ranar 12 ga watan wannan watan na Fabrairu ko kuma kafin ranar domin cika wa’adin da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanya.

Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Alhaji Yunusa Mohammed Abdullahi ne ya bayyana hakan biyo bayan yanke kuɗin aikin hajjin bana da hukumar alhazai ta Najeriya ta yi.

A cewar sa, Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ya ba da shawarar, sannan ya buƙaci alhazai da su tunkari jami’an rajista domin yin rajista, bayan sun cika kudaden. Ya ƙara da cewa biyan cikon kuɗin wajibi ne.

Shugaban ya ce waɗanda suka kasa biyan kuɗin aikin Hajjin na iya rasa damar da suke da ita na yin tafiya zuwa ƙasa mai tsarki domin hukumar ta NAHCON ta riga ta ƙayyade wa’adin biyan cikon kuɗin na aikin Hajjin.

Ya ce, “ana sa ran dukkan maniyyatan su gabatar da takardar banki na musamman da zata shaida biyan kuɗaɗen a cibiyoyin rajistar ƙananan hukumomi.”

Malam Salihu ya nanata cewa an haramta yin rajista ta hanyar wakili, kuma wajibi ne mahajjata marasa ƙarfi ko tsofaffi su kasance tare da wani ɗan uwa a duk lokacin da ake gudanar da aikin hajji.

Idan dai ba a manta ba a makon da ya gabata ne Hukumar NAHCON ta sanar da cewa kuɗin aikin Hajjin bana na 2024 na maniyyata daga Arewa baya ga jihohin Borno da Adamawa ya kai Naira miliyan 4.699.

Da yake tsokaci game da ƙarin kuɗin aikin Hajjin, Malam Salihu ya bayyana cewa yin ƙarin ya zama dole saboda wasu abubuwan da suka wuce ƙarfin su, kamar yadda ake samun hauhawar farashin kuɗin ƙasashen waje.

Shugaban hukumar ya nuna jin daɗin sa da fahimta da haɗin kai na maniyyatan jihar, inda ya ba su tabbacin hukumar ta himmatu wajen ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajji cikin nasara.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar tana aiki tuƙuru tare da NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da ingantacciyar hidima ga maniyyata.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?