Back

An ceto ‘yar Chibok mai ciki tare da ‘ya’yanta bayan shekaru 10 a hannun ‘yan Boko Haram

Rundunar ‘Operation Desert Sanity III’ na Operation Haɗin Kai a Arewa-maso-Gabas sun ceto wata ‘yar Chibok mai suna Lydia Simon.

An ruwaito cewa, sojojin Bataliya ta 82 dake ƙaramar hukumar Ngoza, sun ceto Lydia tare da ‘ya’yanta uku a ranar Laraba.

A cewar Zagazola Makama, ƙwararre kan yaƙi da ta’addanci, Lydia wacce ita ce ta lamba 68 a cikin ‘yan matan da aka sace, ta tsere daga sansanin Ali Ngulde da ke tsaunin Mandara inda aka tsare ta tsawon shekaru da dama.

Ta miƙa kanta ga sojojin Bataliya ta 82 dake Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza. ‘Yar Chibok ɗin da aka ceto na da ciki wata biyar kuma ta yi iƙirarin cewa ta fito daga garin Pemi da ke Chibok.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka cika shekaru 10 da mayaƙan Boko Haram suka sace ‘yan mata 276 a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno.

Yayin da 57 daga cikin ‘yan matan suka kuɓuta daga hannun waɗanda suka sace su a cikin kwanakin da suka biyo baya, daga baya kuma an kuɓutar da 16, yayin da aka sako 107, a lokuta daban-daban, ta hanyar tattaunawa.

Gwamnati da sojojin Nijeriya sun yi alƙawarin ceto sauran ‘yan matan da har yanzu suke hannun’ yan ta’addan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?