
A yau Asabar aka fara gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin jihar Kano na mazabu shida, tare da isowar kayayyakin zaben da wuri.
An fara zaben da misalin karfe 7:30 na safe inda aka ga jami’an hukumar zabe ta INEC a rumfunan zabe, Kuma aka fara yin rajista da kada kuri’a a lokaci guda da karfe 8 na safe a rumfunan zabe daban-daban.
An samu fitowar jama’a da dama a kananan hukumomin Kura da Garun Malam.
A karamar hukumar Garun Malam kayan zabe sun iso kan lokaci, kuma jama’a sun fito da wuri domin kada kuri’a.
za a sake gudanar da zaben ne a mazabu 60 na mazabu uku na kujerun majalisar dokokin jihar.
Mazabar sun hada da Kura-Garun Malam, Rimin Gado-Tofa, da Kunchi-Tsanyawa.
An gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a mazabar Rimin Gado da Tofa ba tare da wata tangarda ba.
Jami’an tsaro sun cika a dukkan runfunan zabe, kuma jama’a sun fito gaba daya domin gudanar da aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su.