Back

An ga watan Ramadan a Saudiyya

An ruwaito cewa an ga jinjirin watan Ramadan a ƙasar Saudiyya a yammacin Lahadi, ma’ana 10 ga Maris ita ce ranar ƙarshe ga watan Sha’aban kuma watan mai alfarma zai fara ne a ranar Litinin 11 ga Maris.

Ramadan, wanda kalandar Musulunci ta ƙayyade yana ɗauke da kwanaki 29 ko 30, yana farawa kuma ya ƙare bisa ga ganin jinjirin wata.

A baya dai mahukuntan ƙasar Saudiyya sun yi kira ga musulmi da su duba jinjirin watan Ramadan.

Kotun Ƙolin ta yi kira ga duk wanda ya ga jinjirin watan da ya kai rahoton kotu mafi kusa.

Australia, Malaysia, Philippines da Brunei sun sanar da 12 ga Maris a matsayin farkon watan Ramadan.

Sai dai ƙasar Oman ta sanar cewa zata fara azumin watan Ramadan a ranar 12 ga Maris, Talata, saboda ba a ga jinjirin watan a yammacin Lahadi ba.

Azumin watan Ramadan ɗaya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.

Watan Ramadan wata ne na tara a kalandar Musulunci da ke gudana tsawon makonni huɗu da kwana biyu, a cikinsa ne musulmi a duk faɗin duniya suke yin azumi tsakanin ketowar alfijir da faɗuwar rana, suna addu’ar samun lafiya da shiriya, suna ba da sadaka ko zakka ko shagaltuwa a ayyukan jin ƙai kamar ciyar da marasa galihu da zurfafa tunani don faɗakar da ransu.

Kwanan watan azumi yana canjawa duk shekara saboda kalandar Musulunci ta ginu ne a kan zagayowar wata, don haka lokacin farawa da ƙarshensa ya dogara ne da ganin jinjirin wata.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?