Back

An ga watan Ramadan, za a fara azumi a Nijeriya Litinin, inji Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, ya sanar da cewa za a fara azumin watan Ramadan a Nijeriya ranar Litinin 11 ga Maris, 2024.

Sultan Abubakar, wanda ke riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa a daren Lahadi.

Sanarwar ta biyo bayan ganin jinjirin watan ne a wuri guda a Nijeriya, kamar yadda Kwamitin Ganin Wata na Ƙasa ya bayyana.

“Sarkin yana taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar azumin watan Ramadan na shekara ta 1445 bayan hijira,” inji sanarwar.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya raya kowane musulmi ya samu damar yin wannan ibadar ya kuma ƙara amfanin dake cikinsa.

Tun da farko dai an ga jinjirin watan Ramadan a ƙasar Saudiyya da sauran ƙasashen duniya.

Watan Ramadan wata ne na tara a cikin kalandar Musulunci da musulmin duniya ke lura da shi a matsayin watan azumi da addu’a da tunani da kuma taimakon mabuƙata.

A duk tsawon wata, musulmi suna azumi gab da sallar asuba, zuwa sallar magriba.

Azumi ya ƙunshi kamewa daga ci, sha, shan taba, da jima’i don samun babban “taƙawa”, ko sanin Allah.

“Ya ku waɗanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke a gabãninku, saboda ku koyi taƙawa da aiki na ƙwarai.” 2:183.

Azumi ɗaya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, tare da imani, da salloli biyar, da sadaka, da gudanar da aikin hajji a Makka – wurin da ake ibadar Musulunci mafi tsarki, wato Ka’aba – ga mai ƙarfin jiki da kuɗi.

A cikin wannan lokacin, Musulmai sun guji ci, sha da jima’i tun daga fitowar rana har zuwa faɗuwar rana na kwanaki 29 ko 30 – ya danganta da lokacin da aka ga sabon jinjirin wata.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?