Back

An Jefa Dan Shekaru Saba’in A kurkuku saboda kashe dansa Dalilin Cinye Sauran Abinci 

Wani dattijo mai shekaru Saba’in Mai suna Theophilus Udeh, a yanzu haka yana hannun ‘yan sanda bisa zargin kashe dan shi, Sunday, dalilin cinye sauran abinci da aka rage a gidan a Eziama Lokpaukwu cikin karamar hukumar Umunneochi ta jihar Abiya.

Da take tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Maureen Chinaka, ta ce, “A ranar ishirin da shida ga wannan watan, hedikwatar ‘yan sanda ta Isuochi ta samu labarin cewar, Theophilus Udeh, Wani mutum dan shekara saba’in daga Eziama Lokpaukwu Umunneochi, ya harbe dan shi, Sunday Udeh, mai shekaru ashirin da shida da haihuwa a ranar ishirin da biyar ga watan nan.

“Bayan samun wannan labarin, jami’an bincike daga hedikwatar sashin Isuochi sun ziyarci wurin da laifin ya faru, inda suka kwashe, tare da ajiye gawar Sunday a dakin ajiyar gawarwaki domin binciko gaskiyar lamarin. Bayan da aka yi bincike an samo wasu hujjoji daga baya kuma aka kama wanda ake zargin.

“An mayar da shari’ar zuwa Sashen Binciken Laifukan Jiha don yin bincike mai zurfi.” Inji ta.

Majiyoyi sun ce Udeh bai ci abincin shi da safe ba, da ya dawo gida yana jin yunwa domin ya ci abincin, sai ya taras cewa marigayin ya riga shi dawowa, ya kuma cinye ragowar abincin da aka bari a cikin tukunya da ke cikin kicin, wanda dan na shi ba shi da sanin cewa abincin mahaifin shi ne aka rage.

Daga nan sai wanda ake zargin ya shiga cikin dakin shi ya fito da bindigar shi ya harbi dan na shi a ka, inda ya mutu nan take.

Majiyar ta ci gaba da cewa, nan take ‘yan unguwar suka kama mahaifin na shi suka daure hannuwan shi suka dora shi a kan gawar dan na shi a dandalin kauyen.

Theophilus wanda aka gani a wani faifan bidiyo da aka yada, ya yi nadama tare da rokon a yi masa afuwa yayin da ya dora alhakin abin da ya aikata a kan daga shaidan ne, inda ya bayyana cewa ya yi nadamar abin da ya aikata.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?