Back

An kama ɗan China bisa zargin kashe wata mata a Abia

An kama ɗan ƙasar China, Gz Zhen, bisa zarginsa da hannu a mutuwar Ocheze Ogbonna, ɗaya daga cikin ma’aikatansa da ke aiki a matsayin mai sarrafa injin ɗaga manyan kaya.

Ana zargin ɗan ƙasar Chinan ne wanda ya so ƙulla alaƙa da Ocheze da kashe ta.

Chris Nkwonta, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Ukwa Gabas/Ukwa ta yamma a Jihar Abia a Majalisar Wakilai, ya ce marigayiyar ta mutu ne bayan da wani ɗan kasar China da ke aiki a Kamfanin Inner Galaxy Steel dake Umuahala-Obuzor ya tura ta daga injin ɗaga manyan kaya saboda ta ƙi amincewa da soyayyarsa.

Ɗan Majalisar ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan mutuwar ‘yar mazaɓarsa, Ocheze, yana mai bayyana matakin da ake zargin ɗan ƙasar Chinan da ɗauka a matsayin mugun abu.

Amma da yake mayar da martani, Kamfanin Inner Galaxy Steel, a wata sanarwa da Mista Ceng Jing, Manajan Hulɗa da Jama’a ya fitar a ranar Laraba ya yi watsi da zargin.

Jing ya ce marigayiya Ocheze ta yi barci ne a lokacin da take sarrafa injin, lamarin da ya kai ta ga faɗowa daga injin.

A halin da ake ciki, bayan faruwar lamarin, matasa a yankin sun yi kira da a kama Zhen, wanda shi ne manajan Inner Galaxy.

Jami’ar Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abia, Maureen Chinaka, ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?