Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Roland Raymond.
Rundunar ta bayyana hakan ta shafin ta na X.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, an kama Raymond, mazaunin ƙauyen Detti da ke ƙaramar hukumar Ganye a lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa.
Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta kuma ce an cafke wanda ake zargin mai shekaru 32 da haifuwa tare da haɗin gwiwar mafarauta.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani Roland Raymond mai shekaru 32 da haihuwa, mazaunin ƙauyen Detti, ƙaramar hukumar Ganye, bisa laifin barazana mai alaƙa da garkuwa da mutane.
“An kama wanda ake zargin ne biyo bayan ƙarar Alhaji Yahaya Kongo da Abraham Paul, inda suka bayyana cewa wanda ake zargin ya kira su ta wayar tarho inda ya buƙaci a biya naira 600,000 ko ya sace su.
“Bayan samun koke-koken, ‘yan sandan da ke yankin Ganye, tare da haɗin gwiwar mafarauta, sun yi gaggawar taruwa tare da cafke wanda ake zargin a wajen karɓar kuɗin da ya nema.
“Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan bincike.”
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watanni biyu da jami’an tsaro suka kamo masu garkuwa da mutane a wurin karɓar kuɗin fansa.
A cikin watan Fabrairu ne dakarun bataliya ta 93 da ke ƙarƙashin 6 Brigade na rundunar sojin Nijeriya suka kama wata mata mai suna Janet Igohia mai garkuwa da mutane a jihar Taraba kamar haka.
Sojojin sun ce an kama Igohia ne a lokacin da take ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa da ‘yan uwan wani da aka sace a Taraba suka biya.