Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, sun cafke wata ‘yar shekara 20 mai sana’ar gyaran gashi mai suna Josephine Odunu da wani direba mai suna Edesemi Ikporo mai shekaru 30 da haihuwa bisa laifin sayar da cin-cin da aka haɗa da miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban makaranta da kuma a bukukuwa a Yenagoa, jihar Bayelsa.
Mista Femi Babafemi, Daraktan Yaɗa Labarai da Bayar da Shawarari na hedikwatar NDLEA, Abuja ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa.
Ya ce jami’an NDLEA da ke sintiri a unguwar Opolo da ke Yenagoa a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris, sun kama direban da ke tuƙa babur, Edesemi, tare da ƙwato giram 200 na cin-cin da aka samar da tabar wiwi, wanda ya je ya kai wa wani mai saye.
“Aikin bin diddigi cikin gaggawa ya kai ga kama mai gyaran gashi, Josephine, wacce take raba cin-cin ɗin daga shagon gyaran gashin da take aiki a yankin Kpansia na Yenagoa.
“Binciken da aka yi a cikin shagon ya kai ga samun kilogiram 3.00 wanda ya kawo jimlar haramtattun kayan da aka kama daga hannun su biyun zuwa 3.2kg.
“Bincike ya nuna cewa suna rarraba cin-cin ɗin da aka haɗa da tabar wiwi da tramadol ga ɗalibai da kuma a wajen bukukuwan ranar haihuwa,” inji Babafemi.
Yayin da Edesemi ke kula da isarwa ga masu siye, Josephine ita ce babban mai rarrabawa ga wanda ake tuhuma wanda ke samar da cin-cin ɗin da ake haɗawa da ƙwayoyin.