Back

An kama masu satar raguna 3, an dawo da raguna 132 a Neja

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wasu mutane uku, Mohammed Abdullahi Chumo (30), Aliyu Salihu (20) da Arzika Ahmadu (25) bisa zargin satar raguna 132.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a garin Zungeru tare da haɗin gwiwar ‘yan banga, kuma a yayin da ake yi musu tambayoyi sun amsa cewa sun haɗa baki tare da yin satar raguna 132 na wasu mutane biyu da ke kiwo a yankin Manigi da ke ƙaramar hukumar Mashegu.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne lokacin da ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa ya hango Chumo a kasuwar Zungeru da ragunan guda shida a lokacin da yake ƙoƙarin sayar da su.

Ya bayyana cewa, “An kama wanda ake zargin, inda ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa ƙauyen Jimi inda aka ajiye sauran raguna, kuma an kama Aliyu da Arzika.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?