Back

An kama motocin abinci guda hamsin da za a fitar zuwa Jamhuriyar Nijar a Zamfara

A ranar Litinin din da ta gabata ne Hukumar Sufuri ta Jihar Zamfara ta kama manyan motoci hamsin da ke jigilar kayan abinci daga Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar.

Hukumar, wacce ke aiwatar da umarnin shugaban kasa da ke da nufin kawo karshen matsalar karancin abinci da boye kaya ce ta kama motocin da ke cike da hatsi iri-iri.

 A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci mutane uku masu baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da sufeto janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun da kuma babban daraktan ma’aikatar harkokin gwamnati Yusuf Bichi da su hada kai da gwamnonin jahohi su dakile boye kayan abinci.

An dauki matakin ne a yayin ganawar da shugaban kasar ya yi da gwamnonin a Abuja kan matsalar karancin abinci da ake fama da ita a halin yanzu sakamakon hauhawar farashin man fetur bayan cire tallafin man fetur da kuma kasa girbin amfanin gonakin noma saboda ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce ta dakatar da tireloli goma sha biyar da ke jigilar kayan abinci ta kan iyakokin Sokoto zuwa Jamhuriyar Nijar.

Kazalika, gwamnatin jihar Kano ta rufe katafaren shaguna da ake zargi da boye kayan abinci har guda goma.

Da yake tabbatar da kama manyan motocin guda hamsin a Zamfara, Shehu Sani, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa, an tare motocin ne a kauyen Gidan Jaja, wanda gari ne da ke iyaka da Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Kakakin hukumar kula da ababen hawa na Jihar, ZAROTA, Sale Shinkafi, ya ce, ana zargin motocin ne da yunkurin fita da kayan abincin zuwa ƙasar ya Nijar ba bisa ka’ida ba. 

Ya ce, “Mutanen mu sun tare motoci guda hamsin makil da hatsi iri-iri a lokacin da suke kokarin fitar da kayan zuwa waje daga kasar. Mun umurce su da su koma su sayar wa ‘yan Nijeriya kayayyakin a kan farashin da ya dace.”

Shinkafi ya bayyana cewa motocin ba su da rakiyar jami’an hukumar amma an umurce su ne kawai su koma yankunan su, su sayar da kayayyakin a farashi mai sauki.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?