Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta ce ta kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a kisan jami’anta a wani aikin bincike a yankin Ughelli da ke jihar Delta.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.
Ya ce an yi wa jami’an da ke aikin binciken a ranar 23 ga watan Fabrairu, kwantar ɓauna yayin da wasu da ke aikin ceto su ma aka yi musu kwantar ɓauna, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda shida.
Adejobi ya ce kamen ya biyo bayan wani gagarumin bincike da jami’an ‘yan sandan suka yi.
A cewarsa, an fara cafke mutane biyar da ake zargi jim kaɗan bayan faruwar lamarin yayin da aka kama wasu ƙarin uku a wurare daban-daban.
Ya ce kama waɗannan ƙarin ukun ya biyo bayan bayanai da haɗin kan waɗanda aka kama da farko.
Adejobi ya ce a halin yanzu waɗanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda, inda suke taimakawa wajen gudanar da bincike.
Ya ce rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta duƙufa wajen ganin an kama duk waɗanda ke da hannu wajen aikata kisan kai da sauran laifuka makamantansu tare da gurfanar da su gaban kuliya cikin gaggawa.
Kakakin ‘yan sandan ya ce nan ba da jimawa ba waɗanda ake zargin za su yi zaman su a kotu, tare da ƙwararan hujjoji, da zarar an kammala bincike.
Ya ce rundunar ‘yan sandan ta yi matuƙar baƙin ciki da wannan ɗanyen aikin na cin zarafin da aka yi wa jami’anta da ke gudanar da ayyukansu na karewa da yi wa al’umma hidima.
“Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da iyalan jami’an da suka mutu a wannan mawuyacin lokaci.
“Muna so mu sake jaddada cewa waɗanda suka kashe jami’an mu a cikin wannan halin da ake ciki da kuma wasu da yawa, sun kashe zaman lafiya kuma babu ɗaya daga cikinsu da zai tafi ba tare da hukunci ba,” inji shi.
An kashe jami’an waɗanda ke bakin aiki a yankin Ughelli na jihar a ranar 23 da 26 ga watan Fabrairu, yayin da wasu shida suka ɓace.