Wani matashi wanda ba a bayyana sunan sa ba, ya shiga bankin UBA da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, ɗauke da bam, inda ya buƙaci naira miliyan 100 don kada ya tayar da bam ɗin.
Wani ma’aikacin bankin da bai so a ambaci sunansa ya bayar da cikakken bayani kan lamarin.
Ya ce hakan ya faru ne a lokacin da ma’aikatan bankin ke halartar kwastomomi, a ranar Litinin.
A cewar majiyar, wanda ake zargin ya tunkari wani mai karɓa da bayar da kuɗi a bankin, inda ya yi kamar zai karɓa kuɗi, amma sai ya baiwa ma’aikacin wata takarda.
Ya faɗa wa ma’aikacin cewa an maƙala bam a jikinsa kuma zai tayar da shi idan ba a biya buƙatarsa ba.
“Da fahimtar buƙatar wanda ake zargin, ma’aikacin bankin ya yi gaggawar sanar da mai kula da su halin da ake ciki, inda nan take ya sanar da jami’an tsaron bankin su buɗe hanyar fita na gaggawa don mutane su gudu. Bayan haka, an sanar da kwastomomi da su bar zauren bankin domin kare lafiyarsu.”
“Da sanin cewa kwastomomi sun fara guduwa ta baya, shi ma ya bi su amma jami’an tsaron bankin suka kama shi, inda daga baya suka kira rundunar katse bam. Da isar su, sai suka kai shi ofishin ‘yan sanda na Rantya domin gudanar da bincike,” inji jami’in.
Ya ce wanda ake zargin ya samu shiga bankin ne saboda bam ɗin da aka maƙala a jikinsa na bogi ne, domin da ƙofar Mantrap ta gano shi idan na asali ne.
Akwai rahotannin cewa wasu fusatattun mutane sun so kashe shi amma jami’an tsaro suka hana hakan.