Back

An kashe basarake a fadarsa a Taraba

Alhaji Abdulmutalib Jankada, basaraken masarautar Sansani a ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba ya rasu.

Wasu ‘yan bindiga da suka kai farmaki fadarsa ne suka kashe shi a daren Alhamis.

A cewar shaidu, maharan da suka shiga garin Sansani a kan babura, sun kutsa cikin fadar ne inda suka harbi basaraken.

An ruwaito cewa ‘yan bindigan sun je wani ɗaki da Sarkin ke zaune, inda suka harbe shi kuma suka ƙwace wayoyinsa daga baya.

An gano cewa sarkin ya mutu nan take.

Wani mazaunin garin Sansani mai suna Musa Sansani ya ce sun ji ƙarar harbe-harbe amma ba su san harbin daga fadar ba ne.

“Marigayi basaraken ya shaida mana cewa zai yi tafiya zuwa Ibbi ne domin bikin kamun kifi na Nwonyo wanda ke gudana a ranakun Juma’a da Asabar. Ba mu san Sarkin bai yi tafiya a jiya da yamma ba don haka da muka ji ƙarar harbe-harbe, ba mu yi zargin a cikin fadar ba ne,” inji shi.

Ya ce ‘yan bindigar sun bar garin cikin sirri bayan sun kashe sarkin kuma matar sa ce da ta same shi a cikin ɗakinsa ya mutu ta sanar wanda hakan ya jawo hankulan jama’ar garin da sauran garuruwan masarautar.

An taɓa sace marigayin a hanyar Jalingo zuwa Wukari shekaru biyu da suka gabata kuma an biya kuɗin fansa kafin a sake shi.

Adadin sarakunan da ‘yan bindiga suka kashe a jihar ya kai bakwai a cikin ‘yan shekarun nan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?